Kwartanci: An anjiye ma'aikacin gwamnatin jihar Katsina a gidan kaso

Kwartanci: An anjiye ma'aikacin gwamnatin jihar Katsina a gidan kaso

Wani ma'aikacin gwamnati da ke jihar Katsina, Abdurahman Ibrahim ya jefa dibo ruwa dafa kansa bayan ya aikata laifin zina da wata matan aure, Hauwa'u Dikko a gidan mijinta da ke Turaruka Quarters da kuma Batsari duka a Katsina.

Ibrahim da ke zaune a Unguwar Allkali Quaters da ke Batsari ya amsa laifin aikata zinar bayan an gurfanar da shi gaban Alkalin kotun Majistare da ke Katsina inda kotun ta umurci a bashi matsuguni a gidan yari kafin a yanke masa hukunci a ranar 4 ga watan Oktoban 2018.

An damke wani ma'aikacin gwamnati a Katsina da ke kwartanci da matar aure
An damke wani ma'aikacin gwamnati a Katsina da ke kwartanci da matar aure
Asali: Twitter

An bayyanawa kotu a ranar Litinin cewa Ibrahim ya saba sulalewa gidan cikin gidan auren Hauwa Dikko da ke Turaruka Quarters domin yin zina da ita ko kuma wani lokaci ta same shi a gidansa da ke Batsari.

DUBA WANNAN: Kotu ta gayyaci Sanatan Najeriya a kan amfani da cheque din banki na bogi

Mijin Hauwa'u, Abubakar Kankiya ne ya shigar da kara a ofishin 'yan sanda da ke Katsina a ranar 12 ga watan Satumban 2018.

Dan sanda mai shigar da kara, Inspecta Sani Ado ya karanto cewa wanda ake karar ya yiwa mai gidan Hauwa butulci inda ya rika saduwa da matarsa a bayan idonsa.

Alkalin Kotun, Hajiya Fadike Dikko ta bayar da umurnin a cigaba da tsare Ibrahim har zuwa ranar Alhamis 4 ga watan Ocktoba domin zartas masa da hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel