Rundunar Yansandan jahar Kano ta tarwatsa wasu gungun yan fashi da suka addabi jama’a

Rundunar Yansandan jahar Kano ta tarwatsa wasu gungun yan fashi da suka addabi jama’a

Biyo bayan wasu bayanan sirri da rundunar Yansandan jahar Kano ta tattara, rundunar ta samu nasarar tarwatsa wani gungun gagga gaggan yan fashi da makami da suka fitinin jama’an jahar Kano har da makota, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rundunar yansandan dake yaki da yan fashi, F-SARS ne ta samu nasarar kama yan fashin a lokacin da ta tare wata mota kirar Mercedes Benz ML350 akan titin Hadeja, ashe motar kanta satota aka yi daga garin Maska na jahar Nassarawa.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya rarraba ma makarantun Firamari sabbin babura 107

Daga cikin wadanda ke cikin motar akwai Kenneth Adam, Ali Jafaru, Abdulkadir Shaka da Aliyu Audu, mazauna garin Masaka na jahar Nasarawa da rukunin Gunduwawa na jahar Kano, kamar yadda kaakain Yansanda SP Magaji Majia ya tabbatar.

Rundunar Yansandan jahar Kano ta tarwatsa wasu gungun yan fashi da suka addabi jama’a
Yan fashi
Asali: Depositphotos

Majiya yace yan fashin sun kai farmaki ne a garin Maska a ranar 22 ga watan Satumba, inda suka kwace ma wani mutumi motar Mercedes Benz ML350 da wasu kayayyaki.

Hakazalika Majia yace sun samu nasarar kama wasu tarin ganyen wiwi a unguwar Tudun Wazirchi da unguwar Badawa na jahar Kano, wanda acewarsa darajar wiwin ta kai naira miliyan 6.6.

A wani labarin kuma, DSP Majia ya bayyana cewa a ranar 19 ga watan Satumba da misalin karfe 3 na rana sun kama wasu matasa guda biyu Dangaja da Lado a yayin da suka tare wani mutumi akan titin Audu Bako inda suka kwace masa kudi naira dubu dari biyar, sa’annan suka raunatashi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel