Abubuwa 4 da zasu taimaka ma Nuhu Ribadu a takararsa ta gwaman jahar Adamawa

Abubuwa 4 da zasu taimaka ma Nuhu Ribadu a takararsa ta gwaman jahar Adamawa

A yayin da babban zaben shekarara 2019 ke cigaba da karatowa, yan siyasa na ta sake sake tare da kulle kulle domin ganin dabarunsu sun kaisu ga gaci, da kuma ganin sun ribaci alakarsu da masu kada kuri’a, iyayen jam’iyya da kuma masu ruwa da tsaki.

Legit.ng ta ruwaito daga cikin masu muradin taka takarar a zaben shekarar 2019 akwai Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, dake muradin darewa kujerar gwamnan jahar Adamawa.

KU KARANTA: Karshen tika tika tik: Gwamna Kashim Shettima ya fatattaki kwamishinoninsa

Da wannan ne muka kawo muku wanu muhimman abubuwa da suke baiwa Nuhu Ribadu kwarin gwiwar shiga wannan takara, duk da cewa akwai gwamna mai ci, Bindow Jibrilla kuma daga jam’iyyar APC shima. Wadannan dalilai sun hada da;

Abubuwa 4 da zasu taimaka ma Nuhu Ribadu a takararsa ta gwaman jahar Adamawa
Ribadu da Buhari
Asali: Twitter

1- Duk wanda ya san Nuhu Ribadu ya san shi a matsayin mutumi mai tsantsani, gaskiya da rikon amana da kuma uwa uba shahararre ne wajen sanin dabaru da salon yaki da rashawa, don haka masana siyasar jahar Adamawa ke kyautata masa zato da cewa yana da kwarewa wajen iya tafiyar da mulki.

2- Dalili na biyu shine wanda ya danganci umarnin da uwar jam’iyyar APC ta aika ma jam’iyyar APC reshen jahar Adamawa na haramta ma shuwagabannin APC ta jahar kada kuri’a a zaben fidda dan takarar gwamnan jahar a inuwar jam’iyar APC da zai gudana a ranar Asabar mai zuwa.

Don haka ake ganin rashin shigar shuwagabannin APC zai bada damar yin zaben gaskiya da gaskiya, inda masana ke ganin Nuhu Ribadu zai iya kai bantensa musamman tunda yana da goyon bayan tsohon sakataren gwamnati Babachir David da Murtala Nyako tsohon gwamnan jahar.

3- Idan za’a iya tunawa, tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu ya tsaya takarar gwamnan jahar Adamawa a zaben shekarar 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, inda ya fafata da Gwamna Bindow, amma bai samu nasara ba inda ya zamo na biyu, haka zalika ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2011 a inuwar ACN, hakan na nufin ya samu gogewa game da siyasar Najeriya, don haka zai iya kai bantensa cikin ruwan sanyi.

4- Sakamakon matsayi da mukaman da Nuhu Ribadu ya rike a baya, hakan yasa ya san mutane da dama wadanda a yanzu haka sune shuwagabannin jam’iyyar APC, don haka suna bashi goyon baya, daga cikin ire iren mutanennan akwai gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ko a satin daya gabata an hangi Ribadu tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a wata ziyara daya kai masa Villa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel