Buhari ya nada sabon shugaban hukumar NIWA

Buhari ya nada sabon shugaban hukumar NIWA

- Shugaba Muhammadu ya nada Sanata Olorunimbe Mamora a mastayin Manajin Direkta na NIWA

- Sanata Olorunimbe Mamora jigo ne a jam'iyyar APC da ya wakilci Legas ta Gabas a majalisa daga 1999 zuwz 2003

- Olorunimbe Mamora kuma ya kasance Kakakin majalisar jihar Legas daga shekarar 2007 zuwa 2011

Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban NIWA
Shugaba Buhari ya nada sabon shugaban NIWA
Asali: Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon Sanata mai wakiltar Legas ta Gabas, Sanata Olorunimbe Mamora a matsayin shugaban hukumar kula da hanyoyin ruwa kas National Inland Waterway (NIWA).

DUBA WANNAN: Dan takarar APC a Kwara ya tona asirin cin hancin da Saraki ya yi masa alkawari idan ya bi shi PDP

Sanarwan nadin na dauke ne a wata wasika daga Ma'aikatan Sufuri na Tarayya da aka aike a ranar 24 ga watan Satumban 2018 mai lamba T.4316/S.63/T/111 zuwa ga Famanen Sakataren hukumar, Mr Sabiu Zakari domin sanar da shi nadin.

A cewar Zakarai, Sanata Olorunimbe Mamora zai fara aiki nan take ne kuma hukumar za ta fara bashi dukkan hakokin da ake bawa ma'aikatan NIWA.

Kafin nadinsa, Mamora jigo ne a jam'iyyar APC kuma shine kakakin majalisar jihar Legas daga ranar 2 ga watan Yunin 1999 zuwa 30 ga watan Mayun 2003.

Ya kuma kasance Sanata mai wakiltan Legas ta Gabas daga 29 ga watan Mayun 2007 zuwa 6 ga watan Yunin shekarar 2011.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel