Dan takarar shugaban kasa: Zan kori duk manyan sojoji daga aiki

Dan takarar shugaban kasa: Zan kori duk manyan sojoji daga aiki

- Da ina da dama, da na kira kowane Janar na rundunar sojojin Najeriya

- Suna tara dukiyar haram ta hanyar cutar da kananan sojoji da yan Najeriya

- Basa yin komai ta bangaren kare kasar mu

Dan takarar shugaban kasa: Zan kori duk manyan sojoji daga aiki
Dan takarar shugaban kasa: Zan kori duk manyan sojoji daga aiki
Asali: Depositphotos

Mahadin kungiyar TakeltBack kuma Chiyaman din jam'iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, yace da yana da dama, zai kori duk janarorin rundunar sojojin Najeriya domin tabbatar da tsaron kasar nan.

Mai neman kujerar shugabancin kasar yace, manyan sojojin sun kasa tsare kasar. Suna tara dukiya ne ta haram ta hanyar cutar kananan sojoji da yan Najeriya.

"Akwai tabbacin cewa janarorin basa komai domin kare kasar nan ko samar wa da kananan sojojin masu hazaka kayan aiki. Karin girma yanzu ya zama siyasa. Shugabanci yanzu yana kewaye da rashawa ne,da yawa daga cikin su suna da gidaje a Dubai da sauran kasaitattun wurare bayan rayukan yan Najeriya na cikin gareni." inji Sowore.

"Yakamata a tambayi sojojin nan yanda aka sace daruruwan yara mata, kuma wadanda suka sace su suka dawo har cikin gari da kansu suka kawo su. Ina suke kai biliyoyin kudaden da ake badawa don tsaron kasa har ta kai ga kananan sojoji na neman abinci da gurin kwana daga mutane?"

DUBA WANNAN: Za'a yi gwanjon kamfunna 10

"Muna da bukatar sauke wadannan manyan domin samar da tsaro ga yan kasar nan. Muna bukatar gwamnati mai sauraron ra'ayin mu domin samar da walwala ga rundunonin mu. Makamai ma akwai bukatar su. Zamu kawo karshen Boko Haram a maimakon aikin hadaka da yan ta'addan sannan kuma Shugabanci ga sojojin zai zamo saboda kwazo ne, ba don siyasa ba. Mata da maza masu kwazo zasu jagoranci rundunonin kasar mu." inji Sowore.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel