Yanzu-yanzu: Ma’aikatan gwamnati zasu shiga yajin aiki ranan Alhamis

Yanzu-yanzu: Ma’aikatan gwamnati zasu shiga yajin aiki ranan Alhamis

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta alanta tafiya yajin aikin ma’aikatan gwamnatin Najeriya na tsawon kwanaki bakwai daga safiyar Alhamis, 27 ga watan Satumba.

A safiyar yau Talata, 25 ga watan Satumba, shugaba kungiyar kwadago ta NLC, Ayuba Wabba, ya tura sakonni ga dukkan abokan aikinsa kan su sanar da mambobinsy a fadin kasa kan yajin aikin da zasu fara ranan Alhamis.

Wabba ya sanar da abokan aikinsa cewa duk da wa’adin kwanaki 14 da suka baiwa gwamnatin tarayya, har yanzu gwamnati tayi banza da su.

Shugaban NLC ya kara da cewa gwamnati bata nuna niyyar sulhu kan al’amuran kara albashin ma’aikata ba.

KU KARANTA: Janar AbdulSalam Abubakar, shugaban INEC sun shiga ganawar sirri kan zaben jihar Osun

Ya umurci dukkan sauran kungoyoyin kwadago a fatan tarayya da su umurnin da gaggawa.

Yace: “Inakwana abokan fafutuka, wannan sanarwa ne game da ganawar da kwadago tayi jiya a Legas. Mun lura cewan har yanzu gwamnati ta yi watsi da wasikar da muka tura mata kuma bata amsa bukatanmu ba.”

“Saboda haka, kungiyoyin kwadago sun yanke shawaran shiga yajin aikin kwanaki bakwai fari daga karfe 12 na daren ranan Laraba, 26 ga watan Satumba, 2018."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel