Subhanallahi! Wannan katon ya zakkewa yar karamar yarinyan nan cikin mota

Subhanallahi! Wannan katon ya zakkewa yar karamar yarinyan nan cikin mota

An damke wani dan kasar Indiya mai shekaru 34 da haihuwaa a daren jiya yayinda yake yiwa wata yar karamar yarinya fyade cikin motarsa a garin Lusaka, kasar Zambia.

Katon ya yaudari yarinyan ne ta hanyar siya mata kaza da dankalin turawa sannan ya shiga da ita cikin motarsa domin tarawa da ita.

Amma yayinda mutane suka ga mota na motsi da kanta, sai suka bude motan suka ga kato kan yar karamar yarinyan yana zufa.

Bayan damkeshi, yarinyan ta bayyana cewa yunwa take ji lokacin da ya saya mata abinci.

An garkameshi a ofishin yan sandan Kabtawa kuma zai gurfana gaban kotu da laifin fyade wa karamar yarinya.

Subhanallahi! Wannan katon ya zakkewa yar karamar yarinyan nan cikin mota
Subhanallahi! Wannan katon ya zakkewa yar karamar yarinyan nan cikin mota
Asali: Twitter

KU KARANTA: Taron Gangamin PDP: Yan takaran da basu son ayi a Ribas makiya Neja Delta ne – Wike ya caccaki yan takara daga Arewa

A bangere guda, mun kawo muku rahoton cewa hukumar yan sandan jihar Gombe ta alanta damke yan ta’addan Kalare 28 kan laifin fyade, fashi da kuma damun jama’a.

Yayinda aka bayyana wadannan yan baranda a jiha, Kwamishanan yan sanda jihar Gombe, Shina Tairu Olukolu, yace hukumar yan sandan ta damkesu ne tare da hadin kan sauran jami’an tsaro.

Yace an damke mutane uku daga cikinsu Abubakar Mohammed, 19; Yusuf Munkaila Dayyabu, 19 bisa ga laifin sace yan mata biyu da musu fyade.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel