Sabon rikici ya barke a tsakanin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP

Sabon rikici ya barke a tsakanin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP

- Sabon rikici ya barke a tsakanin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP

- Rikicin dai bai rasa nasaba da wurin da za'a yi taron gangamin jam'iyyar

- Wasu daga cikin su sun ce basu son Fatakwal

Kawo yanzu dai labarin da muke samu na nuni da cewa an samu sabani a tsakanin kwamitin zartaswa watau National Working Committee (NWC) da kuma kwamitin amintattu watau Board of Trustees (BoT) na jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.

Sabon rikici ya barke a tsakanin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP
Sabon rikici ya barke a tsakanin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP
Asali: UGC

KU KARANTA: Kungiyoyin ma'aikatan mai na shirin tafiya yajin aiki a Najeriya

Sabanin dai kamar yadda muka samu bai rasa nasaba ne da wurin da ake so a gudanar babban gangamin jam'iyyar wanda a wurin ne za'a zabi dan takarar jam'iyyar da zai tunkari zaben 2019.

Legit.ng ta samu cewa a lokacin da yake rantsar da kwamitin gudanar da taron gangamin, shugaban jam'iyyar ta PDP Prince Uche Secondus ya ce a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ne za'a gudanar da gangamin.

Sai dai kuma kamar yadda muka samu, da yawa daga cikin kwamitocin na zartarwa da amintattu su kuma sun bayyana rashin gamsuwa da wurin gudanar da gangamin inda suka zargi ceewa akwai wata makarkashiya da ake shirin kullawa.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kano mun samu cewa sun kai wata mamaya a gidan shugaban kwamitin riko na jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano ranar Litinin din da ta gabata, 24 ga watan Satumba.

Su dai 'yan sandan kamar yadda muka samu, sun je gidan shugaban rikon ne dake a kan titin Sokoto dake garin na Kano inda suka tarwatsa 'ya'yan kwamitin da sauran magoya bayan jam'iyyar ta PDP a jihar Kano dake shirin gudanar da wani taro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel