Jam’iyyar PDP za ta ba Lado Danmarke tikitin Gwamna a Jihar Katsina

Jam’iyyar PDP za ta ba Lado Danmarke tikitin Gwamna a Jihar Katsina

- PDP za ta ba Danmarke tuta a zaben Gwamnan Jihar Katsina

- Danmarke tsohon 'Dan Majalisa ne tun lokacin mulkin 'Yaradua

- Sanatan zai sake gwabzawa da Masari kamar yaddaaka yi a baya

Jam’iyyar PDP za ta ba Lado Danmarke tikitin Gwamna a Jihar Katsina
Masari zai sake karawa da Lado a zaben 2019 a Katsina
Asali: Depositphotos

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa babbar Jam’iyar adawa ta PDP za ta nemi ta tsaida Sanata Lado Danmarke ne a matsayin ‘Dan takarar Gwamna a Jihar Katsina a zabe mai zuwa domin ya kara da Gwamna Aminu Masari.

A wajen wani zaben somin-tabi da Jam’iyyar PDP ta shirya a Jihar Katsina inda kusan kowane babba na Jam’iyar daga Kananan Jihohi 34 sai da ya hallara. A wajen ne aka dauki matakin ba Yakubu Lado Danmarke tuta a zaben 2019.

Shugaban Jam’iyyar na Katsina Alhaji Salisu Majigiri da sauran 'Yan kwamitin da su ka shirya wannan zabe ya bayyana cewa sauran ‘Yan takarar Gwamnan da ake da su za su marawa Sanata Lado Danmarke baya a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: PDP za ta samu nasara a zaben 2019 Inji tsohon Gwamna Kwankwaso

Masu harin kujerar Gwamna Aminu Bello Masari a Jihar Katsina a 2019 sun hada da Abdullahi Umar Tsauri, Musa Nashuni, Abdullahi Garba Faskari, Sada Ilu, Ahmed Aminu Yar’adua da Kabir Kofa sannan kuma shi Sanata Danmarke.

Ana tunanin cewa kusan duka ‘Yan takarar na PDP sun amince da zabin da aka yi na Lado Danmarke sai dai yanzu Magoya bayan Abdullahi Umar Tsauri watau Tuta sun fara kukan cewa an yi amfani da kudi wajen dauko Danmarke.

Masu neman kujerar Gwamnan dai sun zauna ne a Kaduna inda su ka yanke shawarar marawa juna baya. Yakubu Danmarke yayi Sanata ne a PDP daga 2007 zuwa 2011 sannan kuma ya nemi Gwamna a Jam’iyyar adawa ta CPC a zaben 2011.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel