Kwankwaso ya bayyana hikimar da ta sa ya dauko Abba K Yusuf a Kano

Kwankwaso ya bayyana hikimar da ta sa ya dauko Abba K Yusuf a Kano

Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana abin da ya sa ya tsaida Abba Kabir Yusuf a matsayin ‘Dan takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP a lokacin da ya kawo ziyara zuwa Kano.

Kwankwaso ya bayyana hikimar da ta sa ya dauko Abba K Yusuf a Kano
Kwankwaso yace Jama'a za su zabi wanda PDP ta tsaida takara a 2019
Asali: Depositphotos

Sanata Rabiu Musa ya bayyanawa manema labarai cewa Abba Yusuf ne yayi mafi yawan ayyukan da ake gani a cikin Birnin Kano da ma kauyuka a lokacin yana Kwamishinan ayyukan Jihar kuma yana da kishin ganin Jihar Kano ta cigaba.

Kwankwaso ya nuna cewa babu shakka Gwamnatin Ganduje ta gaza yi wa Kanawa aiki ganin yadda abubuwa su ka tsaya a bangeren ginin Jami’ar Jihar da kuma aikin wutan tantarki da hanyoyi da ke Dala da kuma gadar Sabon-Gari.

KU KARANTA: A makon farko da hawa na Gwamnan Kano na kafa Gwamnati - Kwankwaso

A dalilin haka ne tsohon Gwamnan yake ganin za su samu nasara a zabe mai zuwa inda yace abin da jama’a su ke so shi ne a kauda Gwamnatin nan. Sanatan ya nuna cewa ko da ba a ba irin su Sagir Takai tikiti ba, babu matsala a 2019.

Rabiu Kwankwaso yake cewa ‘Dan takarar da ya tsaida watau Abba Yusuf yana cikin wadanda su ka fi kowa takaicin ganin yadda aka yi watsi da irin ayyukan da Gwamnatin sa ta fara don haka yace mutum ne da zai cigaba da yi wa Kano aiki.

A baya dai Kwankwaso ya tsaida Abba Kabir Yusuf da Ahmad Abdulsalam takaran 2019 a Jam’iyyar PDP. Kwankwaso yace ko wa aka tsaida dai dole za a samu wasu sun yi korafi amma su na neman a tafi tare domin kai ga ci a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel