Kudirin kama barayi: Bala Mohammed da Raymond Dokpesi sun kai Buhari Kotu

Kudirin kama barayi: Bala Mohammed da Raymond Dokpesi sun kai Buhari Kotu

Mun ji labari cewa tsohon Ministan babban Birnin Tarayya Abuja Bala Mohammed da wani Jigo a Jam'iyyar PDP Raymond Dokpesi sun kai Gwamnatin Buhari Kotu a dalilin wani kudiri da Shugaban kasar ya kawo kwanaki.

Kudirin kama barayi: Bala Mohammed da Raymond Dokpesi sun kai Buhari Kotu
Raymond Dokpesi da Bala Mohammed sun shiga Kotu da Gwamnatin Buhari
Asali: Depositphotos

Shugaban Kamfanin DAAR Raymond Dokpesi ya maka Shugaban kasa Buhari da kuma Ministan shari'a Abubakar Malami a gaban Alkalin kotun Tarayya na Abuja yana kalubalantar wani kudiri da Shugaban kasar ya sa wa hannu a bana.

Shugaba Buhari ya kawo wani kudiri da zai taimaka wajen maganin barayin kasar nan wanda wasu su ke ganin dokar ta sabawa tsarin mulkin Najeriya. Daga cikin masu kalubalantar wannan kudiri akwai manyan PDP har da irin su Bala Mohammed.

KU KARANTA: PDP ta garzaya Kotu a game da zaben Jihar Osun

Babban Lauya Kanu Agabi SAN ne ya tsayawa masu karar wannan kudiri na Shugaban kasa da kuma Ministan shari’a inda su kace kundin tsarin mulki na 1999 ya ba kowa gaskiya muddin cewa ba a kama sa da wani laifi kuru-kuru a gaban shari’a ba.

Da wannan kudiri dai Shugaban kasar zai damke wasu manya da ake zargi da satar dukiyar jama’a. Agabi yace wannan kudiri na Shugaban kasa Buhari bai yi la’akari da matsayin da dokar kasa ta ba Kotu da masu rike da madafan iko da Majalisu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel