Shugaba Buhari ya sakar ma kungiyar ASUU naira biliyan 20 don gyaran ilimin jami’a

Shugaba Buhari ya sakar ma kungiyar ASUU naira biliyan 20 don gyaran ilimin jami’a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin biyan makudan kudade ga jami’o’in Najeriya na gwamnati da suka kai naira biliyan ashirin (N20,000,000,000) don baiwa kungiyar malaman jami’a damar inganta karatun jami’o’in kasarnan.

Legit.ng ta ruwaito ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta sanar da wannan cigaba a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba a yayin wani taron manema labarai da ma’aikatar kudi ta shirya a Abuja.

KU KARANTA: Mace mau dauke da juna biyu, mijinta, da dansu sun mutu sakamakon abinci mai guba

“Domin tabbatar da ganin an cika wannan umarni na shugaban kasa, na kafa kwamitin gaggawa na musamman a karkashin sakataren kwamitin shugaban kasa na binciken kudi, Dakta MK Dikwa.” Inji Minista Zainab.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a biya tsofaffin ma’aikatan kamfanin jiragen kasa na Najeriya hakkokinsu a naira biliyan 22 da suke bin gwamnatin tun kimanin shekaru goma sha biyar da suka gabata.

A gefe guda kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron koli na majalisar dinkin duniya karo na 73 da zai gudana a cikin satinnan kamar yadda kaakakin shugaban kasa Femi Adesina ya bayyana.

Adesina yace Buhari zai halarci taron ne don tabbatar da matsayin Najeriya game da batun samun dawwamammen zaman lafiya a Duniya, kwace makamai da makaman kare dangi, taimaka ma matasa da mata, magance dumamar yanayi da kuma bin doka da ka’ida tare da kare hakkin biladama

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel