NYSC ta mayar wa da Minista martani: 'Baka yi bautar kasa ba kaima, faqat!'

NYSC ta mayar wa da Minista martani: 'Baka yi bautar kasa ba kaima, faqat!'

- Baka yi bautar kasa ba, baka kuma bi hanyar neman kariya ba

- Matsalar Min istan ta ma fi ta Kemi Adeosun

- 'Ministan ya karya dokar kasa, shima dole ya sauka'

NYSC ta mayar wa da Minista martani: 'Baka yi bautar kasa ba kaima, faqat!'
NYSC ta mayar wa da Minista martani: 'Baka yi bautar kasa ba kaima, faqat!'
Asali: Facebook

Martanin da hukumar NYSC ta mayar wa da Ministan Buhari na sadarwa, Adebayo Shittu, bata zo da mamaki ba, inda tace Ministan ko dai bai san doka ba, ko kuma bai girmama ta ba, kuma bashi da wata kariya a hukumance kan saba dokar.

Adebayo Shitu dai, yace tunda yaci zabe a 1979, yaje majalisa daga jiharsa, ya wadatar ba sai yayi bautar kasa ba, don haka ba zai bar aikin da yake yi na minista ba.

Sai dai kuma, sam sam ba ma irin laifin Kemi Adeosun yayi ba, ganin cewa shi qin yin bautar kasar yayi, inji wasu lauyoyi da majiyarmu ta zanta dasu.

DUBA WANNAN: Za'a biya malaman kaduna hakkokinsu

Mai magana da yawun hukumar, Nike Adeyemi, tace hanyoyi ukku ne kawai ake iya yafe wa mutum bautar kasa a NAjeriya, ko dai cika Shekaru 30 bayan gama makaranta, ko aikin soja na wata tara, ko kuma aiki a hukumomin tsaro.

Ba'a dai sani ba ko shima shugaba Buhari zai ajje shi, ko kuma zai iya zuwa yayi takara a jiharsa ta gwamna, kamar yadda ya nuna sha'awa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel