2019: BPE ta biya bashi har na biliyan daya ga tsofin ma'aikatan NEPA

2019: BPE ta biya bashi har na biliyan daya ga tsofin ma'aikatan NEPA

- An dade da sayar da kamfanin wuta na NEPA

- Sai dai ba'a biya ma'aikatan duka hakkokinsu ba

- Sai yanzu da zabe ya karato wasu ke jin alert

BPE ta biya bashi har na biliyan daya ga tsofin ma'aikatan NEPA
BPE ta biya bashi har na biliyan daya ga tsofin ma'aikatan NEPA
Asali: Facebook

Ofishin dake kula da harkokin sayar da kadarorin gwamnatin Tarayya, watau BPE a Abuja, ya saki biliyan daya ta nairori, kan biyan hakkokin ma'aikatan NEPA wadanda tuntuni suke bin bashi kuma shiru har yanzu ba'a biya su ba.

Zabukan gama-gari dai sun karato, don haka ma gwamnati ke kokan faranta wa ma'aikata da 'yan kasuwa rai, inda ake ta sakin kudaden basuka, don ayyyuka, jari ga matasa, da ma tsohon bashi da gwamnatin ta ja kafa bata biya ba.

Wasu dai har sun mutu basu ji wannan kudi a lalitarsu ba, sai dai magadansu su samu.

DUBA WANNAN: Suruki ya aikata kisan kai

An tantance mutum 480 ne sannan akwai yiwuwar za'a tantance sauran nan gaba suma. Akwai akalla mutum 4,000 da suke bin basuka daga wannan sayar da NEPA da aka yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel