Dalilan da suka sanya aka rage sata da fasa bututan mai a Neja Delta

Dalilan da suka sanya aka rage sata da fasa bututan mai a Neja Delta

- An samu ragowa a satar man fetur

- Bazamu saurarawa duk wanda aka kama da ta'addanci

- Gara su fito neman halastacciyar dukiya

Dalilan da suka sanya aka rage sata da fasa bututan mai a Neja Delta
Dalilan da suka sanya aka rage sata da fasa bututan mai a Neja Delta
Asali: Depositphotos

Kwamandan sojojin ruwa na tsakiya, karkashin rundunar sojojin ruwa ta Najeriya, Rear Admiral Sa'idu Garba, ya bada dalilai uku da suka kawo raguwar satar man fetur a yankin Niger Delta.

Shugaban sojojin ruwan ya lissafo dalilan a Warri a lokacin da ya zagaya bangarorin da ke karkashin shi. Ya jinjiinawa sojojin ruwan da ke bangaren da Kwamandan su, Commodore Ibrahim Dewu.

Garba yace hikimar tsaro uku ne sukayi amfani a bangaren.

"Kamar yanda kuka sani, satar man fetur da sauran ta'addanci sun ragu, daya daga ciki shine aikin 'operation Tsare-Teku' wanda suke tsare hanyoyin ruwa a koyaushe."

DUBA WANNAN: An kashe 'yan shi'a a Yobe

"Na biyu kuma shine rushe duk wasu gine gine da akayi don samar da man fetur ba bisa ka'ida ba."

"Na uku kuma shine hikimar tsare hanyoyin ruwa da toshe duk hanyoyin shige da ficen kayayyaki a yankin."

"Munyi kokarin ganin tsare wadannan hanyoyi uku domin kawo karshen satar mai a bangaren." ya bayyana.

Ya shawarci masu satar mai da su canza salon rayuwa ta hanyar neman halastacciyar dukiya.

Yayi alkawarin ladaftar da duk wanda aka kama da ta'addanci a hanyoyin ruwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel