Zaben gwamnan Osun: Muhimman abubwa 7 da ya kamata ku sani

Zaben gwamnan Osun: Muhimman abubwa 7 da ya kamata ku sani

A yau ne, Asabar, 22 ga watan Satumba, 2018, masu kada kuri’a a jihar Osun zasu zabi sabon gwamna da zai maye gurbin gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, da wa’adin mulkinsa ya kare.

Bayan dukkan jam’iyyu, musamman APC mai mulki da PDP mai adawa, sun kamala yakin neman zabensu, Legit.ng ta kawo maku wasu muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani dangane da zaben nay au, Asabar, 22 ga watan Satumba, 2018.

1. ‘Yan takara 48 ne ke takarar neman maye gurbin gwamna Rauf Aregbesola mai barin gado

2. Adadin mutane 1,687,492 hukumar zabe (INEC) ta yiwa rajisatar zabe a jihar Osun

3. Adadin katin zabe 1,246,915 INEC ta raba

4. Akwai mazabu 332 a jihar Osun

5. Jihar Osun na da kananan hukumomi 30

Zaben gwamnan Osun: Muhimman abubwa 7 da ya kamata ku sani
Manyan 'yan takarar gwamnan Osun
Asali: UGC

6. Hukumar INEC ta raba na’urar tantance masu kada kuri’a guda 4,700

7. Kungiyoyin sa ido na gida da ketare zasu halarci tare da kula da sahihancin zaben

A jiya ne Legit.ng ta kawo maku labarin cewar wani Fasto kuma shugaban Jehovah Power Tabernacle, Prophet Mike Agboola ya yi hasashen dan takarar da zai lashe zaben gwamna da za ayi ranar 22 ga watan Satumban 2018 a jihar Osun.

A yayin da ya ke wa'azi ga mabiyansa a ranar 2 ga watan Satumba, Agboola ya bayyana wanda zai lashe zaben da kuma wanda zai biye masa har ma da na uku inda ya ce Allah ne ya yi masa wahayi.

DUBA WANNAN: 2019: Dalilai 5 da suka sa Tinubu ya juyawa yaronsa Ambode baya

Faston ya yi alfaharin cewa hasashen da ya yi game da zaben gwamna na jihar Ekiti ta zama gaskiya saboda Allah ne ke bayyana masa wadanda za suyi nasarar. Kafin ya bayyana sunayen 'yan takarar da zai lashe zaben, Prophet Agboola ya ce wannan karon zaben zai bawa mutane mamaki domin ba abinda aka saba gani zai faru ba.

Ya ce dan takarar PDP Sanata Ademola Adeleke shine zai zo na uku. Ya ce babban jami'in tsaron gwamna mai barin gado kuma dan takarar APC, Gboyega Oyetola shine zai zo na biyu kana wanda zai lashe zaben shine dan takarar jam'iyyar SDP, Sanata Ishola Iyiola Omisore.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel