Atiku ya kere sauran 'yan takarar jam'iyyar PDP ta fuskar cancantar Shugabanci

Atiku ya kere sauran 'yan takarar jam'iyyar PDP ta fuskar cancantar Shugabanci

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, wata gidauniya a kasar nan ta bayyana mafi cancantar jagoranci cikin dukkanin manema takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP.

Gidauniyar ta Atiku Care Foundation ta bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, shine mafi cancantar shugabancin kasar nan cikin dukkanin manema takarar kujerar shugaban a karkashin jam'iyyar PDP.

Wannan gidauniya ta bayyana hakan ne da sanadin shugabanta na reshen Arewa ta Tsakiya, Golkuna Gotom, yayin ganawa da manema labarai na jaridar Daily Trust cikin birnin Jos a ranar Juma'a ta yau.

Atiku ya kere sauran 'yan takarar jam'iyyar PDP ta fuskar cancantar Shugabanci
Atiku ya kere sauran 'yan takarar jam'iyyar PDP ta fuskar cancantar Shugabanci
Asali: Facebook

Mista Gotom yake cewa, Atiku shine mafi cancantar shugabancin kasar nan da zai jagoranci jam'iyyarsa ta PDP da kuma Najeriya baki daya zuwa tudun tsira.

Ya ci gaba da cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya cancanci kasancewa shugaban kasa sakamakon yadda yankin Arewa maso Yamma ya samu rabonsa na jagorantar kasar nan, inda ya buga misali da tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Yar Adu'a.

KARANTA KUMA: Boko Haram sun kai hari 'Kauyuka 3, rayuka 6 sun salwanta a jihar Borno

A yayin da yake kira domin yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya fitar da shugaban kasa, ya bayyana cewa ba bu mafi cancantar wannan kujera da ya dara Atiku.

A sakamakon shafe tsawon shekaru takwas bisa kujerar mataimakin shugaban kasar nan, Mista Gotom ya furta cewa ba bu mafi cancantar jagoranci cikin dukkanin 'yan takara na jam'iyyar PDP ta fuskar kwarewa da wayewar siyasa da kuma shugabanci.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin gwamnan jihar Kwara na farko na lokacin mulkin Soji, Birgediya Janar David Bamigboyeis, wanda ya riga mu gidan gaskiya a yau Juma'a can jihar Legas bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel