Wani saurayi da ya danne 'yan mata shida ya shiga hannun hukuma

Wani saurayi da ya danne 'yan mata shida ya shiga hannun hukuma

- An kama wani matashi, Chidi Okoye Christain wanda ya dade yana yiwa 'yan makaranta fyade

- Matashin mai shekaru 18 yana amfani da bindiga ne wajen yiwa daliban barazana kafin yi musu fyade

- Mahaifin Okoye ya shaidawa 'yan sanda cewa yaron gagarra hakan ya sa ya gudu daga gida ya shiga duniya

Jami'an 'yan sanda sun damke wani matashi mai shekaru 18, Chidi Okoye Christian da ke zargi da yiwa wasu 'yan matan Jami'ar Jihar Ekiti (EKSU) biyar fyade.

Wanda ake zargin dai ba dalibin makarantar ba ne amma an kama shi tare da abokinsa, Odunmbaku Kayode inda ake same su da wayoyin salula, Katin ATM, bindiga, adda da kuma keken hawa.

Wani saurayi da ya danne 'yan mata shida ya shiga hannun hukuma
Wani saurayi da ya danne 'yan mata shida ya shiga hannun hukuma
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: APC ta kafa kwamitin tantance 'yan takara a matakin tarayya

A yayin da ya ke jawabi a hedkwatan 'yan sanda na Iworoko, Shugaban sashin tsaro na EKSU, Captain Tunde Ajayi (murabus) ya ce Okoye ya yiwa dalibai bakwai fyade cikin watanni uku da suka gabata.

Ajayi ya wanda shine jami'in da ke jagorancin binciken ya ce mafi yawancin daliban da Okoye ya yiwa fyade suna zaune ne a wajen makaranta kuma ya kan yi musu barazana da bindigarsa kafin ya yi musu fyaden.

"Saboda ya san unguwar ciki da wajenta, Okoye na iya fita cikin dare ya aikata mummunan aikinsa kuma ya sulale ya koma dakinsa da ya kwanta inda suke zaune tare da abokinsa Kayode Odunmbaku," inji Ajayi.

Okoye ya amsa aikata laifin fyaden, kuma mahaifinsa ya shaidawa 'yan sanda cewar Okoye gagararren yaro ne domin ya dade da barin gidan iyayenshi saboda irin mummunar halayensa.

Za'a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala bincike inji Ajayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel