2019: Takai yayi watsi da umarnin Sanata Rabiu Kwankwaso

2019: Takai yayi watsi da umarnin Sanata Rabiu Kwankwaso

Mun samu labari daga Daily Nigerian cewa babban ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP Salihu Sagir Takai bai bi umarnin da Sanata Rabiu Kwankwaso ya ba shi ba.

2019: Takai yayi watsi da umarnin Sanata Rabiu Kwankwaso
Takai yayi watsi da Shekarau ya bi Rabiu Kwankwaso
Asali: Twitter

Jaridar ta rahoto cewa Salihu Takai da alamu ya bijirewa Kwankwaso a Kano bayan da ya cigaba da kokarin yakin neman Gwamna a karkashin Jam’iyyar bayan tsohon Gwamnan ya ba shi shawara ya nemi kujerar Sanata a PDP.

Sanata Rabiu Kwankwaso wanda yanzu shi ne Jagoran PDP a Jihar Kano yayi kira ga Salihu Takai da kuma Hafiz Abubakar su hakura da neman Gwamna su nemi kujerar Majalisar Dattawa na Yankin su a zabe mai zuwa na 2019.

KU KARANTA: Karatun mata ya zama kyauta a Jihar Kaduna

Sai dai rahotanni sun nuna cewa manyan ‘Yan siyasan ba su yi na’am da wannan ba inda su ke neman su fito Gwamna domin karawa da Abdullahi Ganduje. Farfesa Hafiz Abubakar dai yayi murabus ne daga Gwamnatin Ganduje kwanaki.

Haka-zalika dai Malam Salihu Takai bai bi tsohon Mai gidan sa Ibrahim Shekerau zuwa APC ba inda ya cigaba da zama tare da tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso a Jam’iyyar PDP yana mai sa ran Jam’iyyar PDP ta ba sa tuta a 2019.

Yanzu haka dai Salihu Takai zai tafi Kaduna inda za a tantance sa a matsayin ‘Dan takarar Gwamna kamar yadda masu yakin neman zaben sa su ka bayyana. Hakan na nufin ba mamaki ‘Dan takarar yayi watsi da shawarar Kwankwaso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel