Aikin jin kai: Gwamna Ganduje ya raba N100, 000, 000 ga wadanda ambaliyan ruwa ya shafa

Aikin jin kai: Gwamna Ganduje ya raba N100, 000, 000 ga wadanda ambaliyan ruwa ya shafa

Gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da bada tallafin naira miliyan dari ga mutanen jahar da ambaliyan ruwa yayiwa barna, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan watsa labaru da al’amuran matasa na jahar Kano, Muhammad Garba ne ya sanar da haka ga manema labaru a ranar Alhamis 20 ga watan Satumba a birnin Kano.

KU KARANTA: Rundunar Yansandan jahar Katsina ta yi ram da wasu matsafa da suka fille kan Dansanda

Kwamishina Garba yace duk dayake dai jahar Kano bata cikin jihohin Najeriya guda goma sha biyu da hukumar bada agajin gaggawa ta yi ma kashedi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohin, amma dai jahar ta samu nata Kason na ambaliyan ruwan.

Kwamishinan ya tabbatar da faruwar ambaliyan ruwa a kananan hukumomin jahar Kano guda takwas, wanda hakan ya janyo mummunan asara da kuma rasher ashen rayukan jama’a da dama.

Kwamishina Muhammad Garba ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasa ransu sakamakon ambaliyan, sa’annan ya gargadi mutane dasu guji gina gidaje akan hanyar ruwa da kuma bakin gabar tafkuna da rafi.

Bugu da kari Muhammed Garba ya jaddada cewa gwamnati na cigaba da yin nazari akan rahoton ambaliyan ruwan daya faru a jahar tare da duba tsananin asarar daya janyo, don haka yayi kira ga gwamnatin tarayya data kawo ma mutanen da abin ya shafa dauki.

Daga karshe Garba yayi kira ga masu ruwa da tsaki dasu hada kai don tallafa ma mutanen da abin ya shafa, tare da duba yiwuwar magance sake aukuwar hakan anan gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel