Wani makaho da mutane 3 sun gamu da ajalinsu a ambaliyar ruwan Delta

Wani makaho da mutane 3 sun gamu da ajalinsu a ambaliyar ruwan Delta

- Akalla mutane 4 ne suka gamu da ajalinsu bayan da ruwa ya ci su a kananan hukumomi 6 na jihar Delta, cikin su kuwa har da wani makaho

- Kananan hukumomi 6 na jihar da ambaliyar ya shafa na kusa da tekun River Niger

- Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutanen guda 4

Akalla mutane 4 ne suka gamu da ajalinsu bayan da ruwa ya ci su a kananan hukumomi shida na jihar Delta, cikin su kuwa har da wani makaho. Jihar Delta na daya daga cikin jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa a cikin jihohi sama da 6 da hukumar NEMA ta zayyana.

Kananan hukumomin da ambaliyar ta yiwa barna sosai a jihar sun hada da Ndokwa ta Gabas, Oshimili ta Kudu, Burutu, Ughelli ta Kudu, Patani da kuma karamar hukumar Bodami, wadanda ke makwaftaka da tekun River Niger.

Wakilin mu ya tattara mana labarin a ranar Labara cewa, ana kyautata zaton makahon na da shekaru kusan 60 da haihuwa, ya mutu ne a lokacin da ya ke kokarin fitowa daga cikin gidansa wanda ya nutse a cikin ruwa, a lokaci da shima ruwan ya ci shi.

KARANTA WANNAN: Kungiyar kwadago ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ko ta shiga yajin aiki

Mutumin wanda ya ke zama a yankin Powerline, a garin Asaba, babban birnin jihar, ya gamu da ajalinsa ne sakamakon dulmiyewar kwale kwalen da ya ke a ciki.

Wani makaho da mutane 3 sun gamu da ajalinsu a ambaliyar ruwan Delta
Wani makaho da mutane 3 sun gamu da ajalinsu a ambaliyar ruwan Delta
Asali: Depositphotos

Wani da lamarin ya afku a gaban sa, Emma Ekube, wanda ya tabbatar da hakan a lokacin da gwamna Ifeanyi Okowa ya ziyarci makarantar firamare ta Ogbe-Afor, daya daga cikin sansanonin wadanda ruwan ya dai-daita su, ya kuma ce yaran mutumin guda 2 sun tsira daga ambaliyar.

Ekube, wanda shine sakataren Al'ummar Powerline, ya bayyana cewa gaba daya yankin nasu ya nutse cikin ruwa wanda ya taso daga tekun River Niger, ya na mai cewa hakan ya tilastawa mutane barin gidajensu zuwa sansanonin gudun hijirar don tsira da rayukansu da kuma sauran dukiyoyinsu da suka rage.

Da ya ke tabbatar da faruwar iftila'in, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasa reshen jihohin Delta da Anambra, Walson Ibarakumo Brandon, ya bayyana cewa bayanan da suke a hannunsu suna nuna cewa mutane uku sun mutu tare da shi makahon na hudu sakamakon ambaliyar ruwan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Wata mata mai shekaru 34 ta haifi yaya 5 a lokaci daya | Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Online view pixel