Muzahara: ‘Yan Shi’a za su cika hanyoyin Garin Abuja yau Alhamis

Muzahara: ‘Yan Shi’a za su cika hanyoyin Garin Abuja yau Alhamis

Mun samu labari cewa a yau Alhamis ‘Yan Shi’an Najeriya za su yi wani gagarumin tattaki a babban Birnin Tarayya na Abuja domin nuna bakin cikin su a wannan Ranar ta 10 ga watan nan watau Ranar Ashura.

Muzahara: ‘Yan Shi’a za su cika hanyoyin Garin Abuja yau Alhamis
Mabiya Shi’a za su yi muzahara a Garuruwan Najeriya yau
Asali: Original

‘Yan Shi’an Duniya dai su kan fito kan tituna su na muzahara a irin wannan rana su na masu tunawa da Jikan Manzon Allah SAW watau Imam Husseini. Yanzu haka kuma babban Malamin Kungiyar IMN ta Shi’a Ibrahim Zakzaky yana daure.

Wannan karo ma dai ‘Yan Shi’a za su yi irin wannan tattaki duk da Gwamnati ta haramta. Wani Jagoran Kungiyar ya nemi Mabiyan sa su fita su cika manyan titunan da ke cikin Birnin Tarayya su na kuma masu kira a saki Malamin su Zakzaky.

KU KARANTA: Tsautsayi ya rutsa da wasu Sojojin Najeriya sun zarce barzahu

A wajen wani babban taro da ‘Yan Shi’a su ka yi kwanan nan, Jagoran Kungiyar ya soki Shugaba Buhari na tsare Malamin su babu gaira babu dalili inda ya kamanta Gwamnatin Buhari da Azzaluman baya kamar yadda mu ka samu labari.

Manyan Malaman Shi’an sun nemi Mabiyan su da su sa bakaken kaya su fita neman shahada a wajen Garuruwan su a wannan Rana ta Ashura su na masu neman Gwamnati ta saki Bajimin Malamin su da aka garkame tun a karshen 2015.

Ku na da labari cewa kwanaki ne Shugaban Kungiyar IMN Ibrahim Yakub Zakzaky yayi kwanaki 1000 a garkame a Najeriya. ‘Yan Shi’a sun yi babban zanga-zanga a dalilin daure Zakzaky da aka yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel