Ba zama: Hotunan ziyarar Osinbajo a kasuwar Nyanya (Abuja) da jaje a Zungeru (jihar Naija)
- A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewar zata fara tallafawa kananan 'yan kasuwa
- A yau, Laraba, ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaddamar da shirin a kasuwar Nyanya dake Abuja
- Bayan kaddamar da shirin bayar da tallafi ga ‘yan kasuwar Nyanya, Osinbajo, ya wuce zuwa garin Zungeru a jihar Naija
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci kasuwar Nyanya dake birinin tarayya, Abuja, domin kaddamar da shirin raba tallafi da gwamnatin Njeriya ke yi ga kananan ‘yan kasuwa a fadin kasa bakidaya.
Bayan ya kaddamar da shirin bayar da tallafin, Osinbajo ya zarce zuwa garin Zungeru a jihar Naija domin ziyarar matsugunin jama’ar da ambaliyar ruwa ta lalatawa muhalli.

Asali: Depositphotos

Asali: Depositphotos
Ko a ranar Alhamis ta makon jiya sai da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaddamar da shirin bayar da tallafi ga kananan 'yan kasuwa a kasuwar Utako dake garin Abuja.
A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewar zata bayar da tallafin kudi maras riba ga kananan 'yan kasuwa.
DUBA WANNAN: Bita-da-kulli: Gwamnan APC mai barin gado ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamna da ya bar mulki tun 2003
A yayin ziyarar, Osinbajo, ya zagaya tare da ganawa da 'yan kasuwar da kuma yi masu tambayoyi. 'Yan kasuwar sun nuna matukar jin dadinsu da ziyarar ta Osinbajo da kuma yadda ya saki jiki da su.
Da yake jawabi ga 'yan kasuwar, Osinbajo, ya ce "tallafin na kanana ne ba manyan 'yan kasuwa ba. Zamu raba N10,000, duk wanda ya biya bayan wata 6 zai samu bashin N15,000, wanda idan mutum ya biya sai ya samu bashin N20,000."

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng