Ajali: Jirgin kasa ya take dan sandan Najeriya da wani dan acaba

Ajali: Jirgin kasa ya take dan sandan Najeriya da wani dan acaba

A safiyar yau ne wani Inspecta na dan sanda, Philip Kolo da wani dan achaba suka rasu bayan jirgin kasa ya markade su.

An gano cewa jami'in dan sandan ya ziyarci Legas ne domin gudanar da bincike kuma yana kan hanyarsa ce ta zuwa Agege domin ganawa da wadanda ya ke gudanar da binciken a kansu.

An samu burbushin babur din da Shogunle in da jirgin kasar ya yi watsi dashi.

Jirgi ya markade dan sanda da wani mutum a Legas
Jirgi ya markade dan sanda da wani mutum a Legas
Asali: Depositphotos

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce tayar bubur din tana kusa da jirgin ne kwatsam sai maginetin jirgin ya janyo babur din da da fasinjojin da ke kai ya markade su.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

Wani shaidan idon ya ce jirgin ya yi horn tun daga nesa kuma mutane da ke wajen sun gargadi dan acaban ya matsa daga layin dogon ya jira jirgin ya wuce amma ya cigaba da tsayuwarsa inda ya ke.

An kuma gano jakar dan sandan da ya taho da ita daga babban birnin tarayya, Abuja.

Kakakin 'yan sanda na jihar, Chike Oti, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa 'yan sandan layin dogo suna gudanar da bincilke kan lamarin.

Oti ya ce dan sandan da ya mutu yana aiki ne da rundunar sanya ido ta sufeta janar din 'yan sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel