Fidda Gwani: Dalilin da ya sanya muka yi watsi da Zaben 'yar tinke - APC Adamawa

Fidda Gwani: Dalilin da ya sanya muka yi watsi da Zaben 'yar tinke - APC Adamawa

A yayin da babban zabe na 2019 ke ci gaba da karatowa, jiga-jigan majalisar dokoki ta tarayya karkashin jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa, sun bayyana goyon bayansu karara na watsi da 'yar tinke yayin zaben fidda gwani kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

A yayin da aka samu rabuwar kai cikin jam'iyyar APC dangane da salo da tsarin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar, jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin kasar nan da suka juya baya kan aiwatar da 'yar tinke yayin zaben fidda 'yan takara.

Kungiyar jiga-jigan jam'iyyar reshen jihar ta Adamawa da ta hadar da 'yan majalisar wakilai 8 da kuma Sanata daya, sun bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan Abuja a ranar Talatar da ta gabata.

Sanatan jihar Adamawa ta Arewa, Binta Garba, ita ta bayyana hakan a madadin sauran 'yan kungiyar masu wakilcin jihar da cewa, sun goyi bayan wannan lamari na aiwatar da zaben ta hanyar wakilan jam'iyya bisa tanadin sashe na 20 cikin dokokin jam'iyyar reshen jihar.

Fidda Gwani: Dalilin da ya sanya muka yi watsi da Zaben 'yar tinke - APC Adamawa
Fidda Gwani: Dalilin da ya sanya muka yi watsi da Zaben 'yar tinke - APC Adamawa
Asali: Twitter

Sanata Binta ta bayyana cewa, kungiyarta ta amince da aiwatar da zaben fidda gwanaye na dukkan kujerun takara na jihar ta hanyar zabin amintattun wakilai in banda na kujerar shugaban kasa da za a aiwatar da shi ta hanyar 'yan tinke.

Ta ci gaba da cewa, daya daga cikin dalilan da ya sanya suka watsar da zaben 'yar tinke a jihar sun hadar da matsalolin tsaro musamman ta'addancin hare-haren Boko Haram da zai hana gudanar zabe cikin wasu yankuna dake gabar Dajin Sambisa a yankunan Arewa na jihar.

KARANTA KUMA: Fitattun 'Yan 'Kwallo 5 da suka tashi cikin Talauci kuma suka zamto Hamshakai

Kazalika Sanata Binta ta bayyana cewa, aiwatar da zaben fidda gwanaye na jam'iyyar cikin jihar ta hanyar wakilai zai kawo sauki batar da dukiya a madadin na 'yar tinke.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, sauran 'yan majalisar masu wakilcin jihar sun hadar da; Sadiq Ibrahim, Yusuf Yakub, Abdulrazak Namdas, Abdulrahman Shu'aibu, Adamu Kamale, Lawal Garba, Philip Gutuwa da kuma Talatu Yohanna.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani jigo na jam'iyyar PDP reshen jihar Nasarawa, John Mamman, ya jagoranci dumbin magoya baya wajen sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tun a ranar Lahadi 22 ga watan Yulin da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel