2019: Jam'iyyar APC za ta fara tantance 'yan takarar ta a yau Laraba

2019: Jam'iyyar APC za ta fara tantance 'yan takarar ta a yau Laraba

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, a yau Laraba jam'iyyar APC ta za ta fara gudanar da muhimmin aiki na tantance 'yan takararkarun ta manema kujeru daban-daban a matakai na jihohi da kuma tarayyar Najeriya baki daya.

Tantancewar da aka kayyade za ta gudana ne daga ranar 19 zuwa ranar Juma'a 21 ga watan Satumba na wanna shekara, inda ake sa ran manema takarar kujerun gwamnoni da kuma majalisar dokoki ta tarayya su gabatar da kansu a shelkwatar jam'iyyar dake babban birnin kasar nan na tarayya domin tantancewa.

Kazalika, jam'iyyar za ta tantance sauran manema takarar kujerun majalisar dokoki na jiha a jihohin su daban-daban dake fadin kasar nan.

Shugaban jam'iyyar APC; Adams Oshiomhole
Shugaban jam'iyyar APC; Adams Oshiomhole
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan yunkuri na tantance manema takarar ya bayu ne bisa ga hukunci na shugaban jam'iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, bayan wata doguwar tattaunawa da kwamitin kusoshin jam'iyyar da ta gudana a daren ranar Litinin din da ta gabata.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya shiga hannu bisa laifin Luwadi da Yara 2 a jihar Katsina

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, jam'iyyar ta kayyade ranar 26 ga watan Satumba domin gudanar da zaben fidda gwani na manema takarar kujerar shugaban kasa, inda za ta fidda gwanayen manema takarar kujerun gwamnonin jihohin kasar nan a ranar 29 ga watan na gobe.

Bugu da kari, jam'iyyar ta kayyade ranar 2 ga watan Oktoba domin fidda gwanayen takarar kujerun sanata da kuma ranar 3 ga watan Okotoba ta fidda gwanayen takarar kujerun majalisar wakilai.

A yayin da jam'iyyar za ta gudanar da taron ta na gangami a ranar 6 ga watan Oktoba, za ta fidda gwanayen takarar kujerun majalisar dokoki na jihohin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel