Wani Matashi ya shiga hannu bisa laifin Luwadi da Yara 2 a jihar Katsina

Wani Matashi ya shiga hannu bisa laifin Luwadi da Yara 2 a jihar Katsina

Za ku ji cewa wani Matashi dan shekara 30 a duniya, Ibrahim Lawal, zai gurfana gaban babbar kotun Majistire dake jihar Katsina a ranar 3 ga watan Oktoba bisa zarginsa da aikata laifi na Luwadi da wasu yara biyu 'yan shekaru takwas.

Lawal, wanda mazaunin unguwar Rafin Sarki ne dake karamar hukumar Bakori, ana kuma zargin sa da laifin yiwa yaran biyu barazanar kawar da su daga doron kasa muddin suka furta wannan mummunan lamari da ya aikata da su.

A halin yanzu dai ana ci gaba da tsare Matashin a gidan kaso yayin zaman kirdado na tsawon lokutan da kotun ta kayyade domin fara sauraron kararsa bisa umarnin Alkaliya Fadila Dikko.

Wani Matashi ya shiga hannu bisa laifin Luwadi da Yara 2 a jihar Katsina
Wani Matashi ya shiga hannu bisa laifin Luwadi da Yara 2 a jihar Katsina
Asali: Facebook

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito, wannan lamari ya fito fili yayin da yaran biyu suka shaidawa iyayensu mummunan abin takaici da ya auku a kansu da nan take suka shigar da rahoto har ga hukumar 'yan sanda.

A yayin binciken wannan lamari, Matashin ya amsa laifin sa ba tare da wata gardama ba da ya sabawa sashe na 284 da kuma na 397 cikin dokokin kasar nan.

KARANTA KUMA: Fulani sun bukaci gwamnatin tarayya ta raba Makiyaya da Makamai

Legit.ng ta fahimci cewa, jami'in dan sanda mai shigar da kara gaban kotun ya bayar da shaidar cewa, kawowa yanzu bincike na ci gaba da gudana kan wannan lamari da ya sanya kotun ta daga sauraron karar har zuwa watan gobe.

A yayin haka kuma mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta cafke wasu matasa 4 a jihar ta Katsina bisa aikata laifi na fashi da makami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel