Siyasar Kano: Kawu Sumaila ya zargi Kabiru Gaya da saba yarjejeniyar da su kayi

Siyasar Kano: Kawu Sumaila ya zargi Kabiru Gaya da saba yarjejeniyar da su kayi

Mun samu labari daga Hukumar dillacin labarai na kasa cewa Alhaji Abdurrahman Kawu-Sumaila, wanda yana cikin masu ba Shugaban kasa shawara ya kai Kabiru Gaya kara wajen ‘Yan Sanda.

Siyasar Kano: Kawu Sumaila ya zargi Kabiru Gaya da saba yarjejeniyar da su kayi
'Yan Sanda za su kira Kabiru Gaya saboda amfani da maakami wajen siyasa
Asali: Twitter

Mai ba Shugaba Buhari shawara kan harkar Majalisa Abdurrahman Kawu-Sumaila ya kai karar Sanatan Kano ta Kudu watau Kabiru Gaya kara gaban ‘Yan Sanda jiya a dalilin sabawa wata yarjejeniya da Sanatan ya saba.

Hon. Abdurrahman Kawu-Sumaila ya kai kukan sa ne gaban Kwamishinan ‘Yan Sanda n Kano Rabi’u Yusuf inda yace Magoya-bayan Sanatan na Kudancin Kano sun yi masa barna lokacin da ‘Dan Majalisar Dattawan ya je kamfe.

Kawu-Sumaila yana zargin wasu Mabiyan Sanata Gaya da rusa masa fastoci a Kudancin Kano lokacin da Sanatan Yankin ya shigo Gari domin yakin neman zabe. Sumaila yace an kuma yi wa wasu mota da babura barna a taron.

KU KARANTA: Jama’a sun yi wa wani Sanata Gaya ihun ‘ba ma so’ a Jihar Kano

Tsohon ‘Dan Majalisar Wakilan wanda yanzu yake harin kujerar Sanata Gaya yace Sanatan na amfani da ‘yan daba kiri-kiri wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar da su kayi a baya na cewa ban da amfani da makamai a siyasa.

Sumaila wanda ke ba Shugaban kasa shawara ya nemi jami’an tsaro su dauki matakin da ya dace bayan Sanatan ya samawa yarjejeniyar da aka yi a baya na yin siyasa cikin tsabta domin ganin an yi siyasa ba da gaba ba a cikin Kano.

Jiya kun ji labari cewa Dattijon nan na Yankin Arewa watau Dr. Tanko Yakassai ya fito ya bayyana dalilin da ya sa ya marawa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan baya a zaben 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel