Sun auna sa'a: Lakcarorin makarantar jihar Kaduna sun kubuto daga hannun masu garkuwa da mutane

Sun auna sa'a: Lakcarorin makarantar jihar Kaduna sun kubuto daga hannun masu garkuwa da mutane

- An sako malaman makarantar jihar Kaduna da aka sace

- Shugaban makarantar ya bayyana hakan

- A ranar Lahadi ne aka sace malaman

Malaman makarantar koyon aikin lafiya dake Makarfi, jihar Kadun ta tunawa da Shehu Idris watau Shehu Idris College of Health, Makarfi a turance har su uku sun kubuta daga hannun masu satar mutanen da suka yi garkuwa da su, kamar yadda majiyar mu ta tabbatar.

Sun auna sa'a: Lakcarorin makarantar jihar Kaduna sun kubuto daga hannun masu garkuwa da mutane
Sun auna sa'a: Lakcarorin makarantar jihar Kaduna sun kubuto daga hannun masu garkuwa da mutane
Asali: UGC

KU KARANTA: Korar da Buhari yayi mun gaba ta kai ni - Babachir Lawal

Wannan dai na kunshe ne a cikin wani sakon kar ta kwana na wayar Salula da shugaban makarantar, Yusuf Yakubu ya aikewa wakilin majiyar ta mu da daren ranar Talatar da ta gabata inda ya bayyana cewa an saki malaman makarantar ne da karfe takwas na dare.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa, Malam Yusuf yace ya samu nasarar kubutar da malaman makarantar tasa ne bayan tattaunawa da kuma shiga yarjejeniya da masu garkuwar.

A jiya dai idan mai karatu bai manta ba kun kawo maku labarin cewa an sace malaman a ranar Lahadin da ta gabata akan hanyar su ta zuwa Makarfi daga garin Zariya.

Waddanda aka sace din dai sun hada da Hajiya Rabi Dogo da Halimatu Malam, sai kuma shugaban tsangayar koyon aikin lafiyar hakori na makarantar Dakta. Akawo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel