Sharhi: Aiki jaa! Gaban sabon shugaban DSS Bichi

Sharhi: Aiki jaa! Gaban sabon shugaban DSS Bichi

- Sabon shugaban DSS Bichi ya sha alwashin maido da sunan ofishin cikin martaba

- Zai fuskanci zaben da tsaron kasa

- Ana sa rai zayyi aiki babu kabilanci

Sharhi: Aiki jaa! Gaban sabon shugaban DSS Bichi
Sharhi: Aiki jaa! Gaban sabon shugaban DSS Bichi
Asali: UGC

A kowacce kasa, ana dauko wanda zai shugabanci hukumar tsaro ne domin ya kula da tsaro na shgaban kasa, gwamoni, zababbu da 'yan majalisu. Sannan kuma aikinsu ne su tsare kasa daga matsalolin tsaro na cikin gida masu zagon kasa.

Daga cikin manyan alkawurra da ya daukarwa ma'aikatansa, Agent Bichi, wanda ya shekara 35 yana wannan aiki, kuma yayi ritaya a bara, yana da kyakkyawar alaka da dangantaka da ma'aikata, wadda ya tabbatar zai inganta, sannan kuma babu kabilanci ko bangaranci a aikinsa.

Abubuwa da zai yi fice a kansu a wannan aikin yanzu sune:

DUBA WANNAN: Dakwalen kaji da Najeriya ta samar wa duniya ta hanyar kimiyya

1. Bayar da gudummawar tsaro kan 'yan takarkaru.

2. Bayar da gudummawar tsaro kan zabuka na 2019

3. Tsaro a wuraren tarukan zabe

4. Tsaron kasa a yaki da ta'addanci

5. Inganta tsaron kasa kan rarrabuwar kawuna na kabilanci da addinanci

6. Gyara a harkar tsaro su daina siyasa

7. Tabbatar da 'yancin jama'a a cikin kasa, ba tare da tauye musu hakki ba

8. Kin sanya kansa a matsayin shugaban bangare na kasa

9. Hada kai da sauran hukumomin tsaro don yada bayanai na sirri don aikinsu ya tafi daya

10. Samar da kayan aiki da kwarewar zamani ga ma'aikata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel