Kwamacala ta kacame kwangilar shirin dabaibaye Najeriya da yanar gizon ganin samaniyar jirage

Kwamacala ta kacame kwangilar shirin dabaibaye Najeriya da yanar gizon ganin samaniyar jirage

- Ana so a game Najeriya da yanar gizon RADAR

- Radar kamar Rediyo take mai ganin ko me ke sararin samaniya

- Ana amfani dashi don gano jirage ko makamai

Kwamacala ta kacame kwangilar shirin dabaibaye Najeriya da yanar gizon ganin samaniyar jirage
Kwamacala ta kacame kwangilar shirin dabaibaye Najeriya da yanar gizon ganin samaniyar jirage
Asali: Depositphotos

Duk kokarin gwamnatin Najeriya na ta samar da takanolojin da zata game kasar nan da yanar gizon Rediyo da zata bada damar ganin ko me ke yayo a sararin saman kasar nan a ko da yaushe ya ci tura.

An so a game kasar kamar yadda aka yi a kasashe da suka ci gaba, amma abin ya gagara, duk da makudan kudade da aka kashe.

Ana so a game Najeriya da yanar gizon RADAR. Ita Radar kamar Rediyo take mai ganin ko me ke sararin samaniya. Ana amfani dashi don gano jirage ko makamai

DUBA WANNAN: Dakwalen kaji da Najeriya ta samar wa duniya ta hanyar kimiyya

An ware Yuro miliyan 67 ne don wannan aiki, an kuma kira aikin da TRACON, watau Nigera Total Coverage by RADAR.

Tun 2003 aka ayyana kwangilar, amma sai a 2010 aka fara aiki a kanta, bayan da tsohuwar hanyar sadarwas ta zama ta tsufa, kuma tashoshi da harkar jirgin sama ke qara bunkasa.

NAMA, hukumar harkokin sufurin sama, ita ke da alhakin wannan aikin, kuma ta baiwa wani kamfanin Faransa da ya kware a harkar ne kwangilar.

Matsalar kayan aiki, kayan gyara da kkayan sapaya na musaya wadanda suka daina aiki shi yake ci ma aikin tuwo a kwarya, inji daraktan hukumar ta NAMA Umar Faruk.

Idan dai jirgi ya fadi ko ya bace, nemansa kan yi wahala idan babu irin wannan kayan aiki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel