Inyamurai ke da'awar akidar Yarbawa ta sauya fasalin Najeriya - Yakasai

Inyamurai ke da'awar akidar Yarbawa ta sauya fasalin Najeriya - Yakasai

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito mun samu rahoton cewa, daya daga dattawan jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana yadda Inyamurai ke ci gaba da dabbaka da'awa ta akidar Yarbawa kan sauya fasalin kasar nan.

Sai dai Alhaji Tanko ya bayyana cewa, wannan akida ta na kunshe ne da manufa ta kitimurmurar wani yunkuri na kawo rikici da rashin zaman lafiya a kasar nan.

Dattijon na jihar Kano ya bayyana hakan ne a yayin wata lacca da cibiyar bincike da cigaban Afirka ta gudanar a Kanon Dabo.

Inyamurai ke da'awar akidar Yarbawa ta sauya fasalin Najeriya - Yakasai
Inyamurai ke da'awar akidar Yarbawa ta sauya fasalin Najeriya - Yakasai
Asali: UGC

Yake cewa, sauya fasalin kasa kamar sauran ra'ayoyi da suke kunshe da matsala, wata akida da ce da Yarbawan kasar nan suka dauka da manufar kawo tasku da barazana ta zaman lafiya a kasar nan.

Alhaji Tanko ya yi kira kan cewa, matukar sauya fasalin kasa yana nufin gyare-gyare cikin kundin tsarin mulki, dole sai an yi shimfidar tsare-tsare da za su tabbatar da wannan lamari ta hanyar amfani da wakilai cikin zababbun 'yan siyasa, wanda a halin yanzu suke shakkar yin wannan kira na gyare-gyare cikin kundin tsarin sakamakon yawan al'ummar dake yankin Arewacin kasar nan.

KARANTA KUMA: 2019: David Mark, Saraki sun raba kan Arewa ta Tsakiya da Majalisar Dokoki ta tarayya

A yayin da wasu mutane ke kira kan sake dabbaka kundin tsari na shekarar 1962 a kasar nan, Alhaji Tanko ya bayyana cewa hakan ba zai tabbatu ba kasawancewar kundin tsari na 1962 ya kunshin yankuna 4 kacal nan kasar sabanin yadda suke yankuna 6 a wannan zamani.

Kazalika dattijon ya kara da cewa, kira gami da dabbaka sauya fasalin kasar nan wani kira ne da zai janyo rabuwar kan al'umma da manufa ta ci gaba da rura wutar adawa dake tsakanin Yarbawa, Inyamurai da kuma Hausawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel