An bawa hammata iska yayin rikicin shugabancin APC a Bauchi

An bawa hammata iska yayin rikicin shugabancin APC a Bauchi

- Jigo a APC na Bauchi, Yakubu Ibrahim, ya yi ikirarin magoya bayan gwamnan jihar sun masa duka

- Ibrahim ya ce an doke shi ne saboda ya ce bai amince da bawa gwamnan jihar tikitin takara ba har sai anyi zaben fidda gwani

- Ibrahim ya ce zai shigar da kara kotu domin an ci masa mutunci kuma an danne masa hakkinsa na bayyana ra'ayinsa a jam'iyyar

Wata sabuwar rikici ta kuno kai a jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi inda daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar, Alhaji Yakubu Ibrahim, ya yi ikirarin cewa magoya bayan gwamna Muhammad Abubakar sun doke shi saboda bai amince da kudirin bawa gwamnan tikitin tazarce ba.

An bawa hammata iska yayin rikicin shugabancin APC a Bauchi
An bawa hammata iska yayin rikicin shugabancin APC a Bauchi
Asali: Twitter

A lokacin da ya ke hira da manema labarai a jiya Juma'a, Yakubu Ibrahim, wanda shine direktan yakin neman zaben daya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam'iyyar, Mohammed Ali Pate, ya ce magoya bayan gwamnan sun kira taro a gidan gwamnan inda suka tsayar dashi a matsayin dan takara ba tare da zaben fitar da gwani ba.

DUBA WANNAN: Dogara ya fadi sharadi daya da zai sa ya cigaba da zama a APC

Ya ce, ya yi kokarin bashi damar ya yi magana a wajen taron domin nuna rashin amincewarsa da matakin da sauran 'yan jam'iyyar suka dauka na zaban gwamna mai ci a matsayin dan takara ba tare da zaben ba amma ba'a bashi ikon magana ba.

A cewarsa, ya tashi daga kujerarsa saboda ya bayyana ra'ayinsa ga Ciyaman din jam'iyyar, Uba Nana amma sai wasu daga cikin 'yan jam'iyyar masu goyon bayan gwamnan suka shake shi, suka rufe shi da duka har sai da suka fitar dashi daga dakin taron.

Yakubu ya ce a halin yanzu ya shigar da kara kotu domin shugabanin jam'iyyar Uba Nana da mataimakin gwamna, Audu Sule Katagum suna zaune suna kalo aka ci masa mutunci aka hana shi fadin ra'ayinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel