Shugaba Buhari ya sawo jirage 30 tun bayan hawan sa mulki a 2015

Shugaba Buhari ya sawo jirage 30 tun bayan hawan sa mulki a 2015

- Shugaba Buhari ya sawo jirage 30 tun bayan hawan sa mulki a 2015

- Hafsan sojojin saman Najeriya Sadiq Abubakar yace haka

Hafsan sojojin saman Najeriya Sadiq Abubakar ya bayyana cewa rundunar sa ta sayi akalla jiragen yaki talatin tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari a karagar mulki kimanin shekaru uku da suka shude.

Shugaba Buhari ya sawo jirage 30 tun bayan hawan sa mulki a 2015
Shugaba Buhari ya sawo jirage 30 tun bayan hawan sa mulki a 2015
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Tikiti a PDP: Saraki ya samu goyon bayan gwamnoni 6

Hafsan sojin dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a yayin bude wasu muhimman ayyuka a makarantar koyon aikin sojan saman ta Najeriya dake a garin Kaduna.

Legit.ng haka zalika ta samu cewa Mista Sadiq Abubakar ya kuma kara da cewa rundunar ta samu sukunin gyara wasu jiragen goma sha takwas duk dai a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

A wani labarin kuma, Jirgin kasan dake jigilar fasinjoji daga garin Abuja zuwa Kaduna a ranar Asabar yayi hadari kan hanyar sa daga garin Abuja zuwa Kaduna jim kadan bayan barin tashar sa dake a unguwar Idu, Kubuwa, birnin tarayya Abuja.

Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa jirgin kasan dai haka zalika ya yi raga-raga da wata baiwar Allah inda ya markade ta ta yadda ba ma a gane ta kwata-kwata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel