Fadar Shugaban kasa ta bude wuta kan Bankin HSBC da ya yi hasashen rashin nasarar Buhari a zaben 2019

Fadar Shugaban kasa ta bude wuta kan Bankin HSBC da ya yi hasashen rashin nasarar Buhari a zaben 2019

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, fadar shugaban kasa cikin fushi da bayyana bacin rai ta mayar da martani kan wani babban banki na kasar Birtaniya, HSBC, da yayi hasashen rashin samun nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Cikin sakamakon wata kiddiga da Bankin ya fitar a wata mujalla ta tattalin arziki tun a watan Yulin da ya gabata, kafofin watsa labarai sun kalato rahoton da cewa, kididdigar ta hikaito yadda jam'iyyar adawa ta PDP za ta lallasa jam'iyya mai ci ta APC a yayin zaben na badi.

Binciken ya bayyana cewa, jagorancin Najeriya na shugaba Buhari a karo na biyu zai matukar dagula al'amurra gami da gurbata ci gaban kasar nan ta fuskar tattalin arziki.

Sai dai cikin wata sanarwa a ranar Asabar din da ta gabata, fadar shugaban kasa ta zargi babban bankin da bayar da kofa bude ta assasa rashawa ta hanyar tallafawa shugabannin kasar nan na da da kuma na yanzu wajen wawushe dukiyar al'umma daga asusun gwamnati.

Fadar Shugaban kasa ta bude wuta kan Bankin HSBC da ya yi hasashen rashin nasarar Buhari a zaben 2019
Fadar Shugaban kasa ta bude wuta kan Bankin HSBC da ya yi hasashen rashin nasarar Buhari a zaben 2019
Asali: Depositphotos

Ta kuma buga misali dangane da yadda babban bankin ya tallafawa tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha, wajen yashe dukiyar kasar nan da ta haura sama da Dalar Amurka Miliyan 100 zuwa rassa bankin dake biranen Jersey, Paris, Landan da kuma birnin Geneva na kasar Switzerland.

KARANTA KUMA: Sanata David Mark ya ziyarci tsohon Shugaban kasa, IBB, a birnin Minna

Fadar ta shugaban kasa ta kuma bayyana cewa, bankin na HSBC na son rusa gwamnatin shugaba Buhari a sakamakon akidar yaki da rashawa da ta sanya a gaba, inda hakan ya hana bankin sakat wajen gudanar da wannan almundahana tare da hadin gwiwar barayin gwamnati na kasar nan.

Ta kuma nemi bankin akan ya yi azamar dawowa da Najeriya kudaden ta da kimanin shugabanni sama da hamsin suka yashe cikin asusun gwamnati na kasar nan kuma suke ajiyarsu a rassa daban-daban na bankin dake fadin duniya.

A yayin da fadar shugaban kasar ke ci gaba da bayyana fushin ta kan wannan babban banki da ya bayar kofa buda ta rashawa a kasar nan, jaridar Legit.ng ta kuma fahimci cewa, fadar ta yi wannan martani ne da sanadin kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel