Kotu ta bayar da umarni kama wasu ‘ya’yan tsohon shugaban kasa

Kotu ta bayar da umarni kama wasu ‘ya’yan tsohon shugaban kasa

Wata kotun kasar Masar (Egypt) ta bayar da umarnin kama yaran tsohon shugaban kasar su biyu; Gamal Mubarak da Alaa Mubarak, domin gurfanar da su a gabanta tare da amsa tambayoyi a kan tuhumar su da yin kwange a kasuwar hada dadar hannayen jari ta kasar.

Kotun na tuhumar Alaa da Gamal tare da wasu mutane 7 bisa zarginsu da karya dokokin kasuwar hada-hadar hannayen jari da babban bankin kasar domin samun haramtacciyar riba.

Wani kamfanin dillancin labarai na yankin gabas ta tsakiya ya bayyana cewar duk da wadanda ake tuhuma din sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da yi, wata majiyar kotu ta tabbatar masu da cewar yanzu haka an kama mutane uku dake aiki a bankin hannayen jari na kasar Masar (EFG).

Kotu ta bayar da umarni kama wasu ‘ya’yan tsohon shugaban kasa
Gamal da Alaa
Asali: Depositphotos

An fara tuhumar ‘ya’yan tsohon shugan kasar Masar, Husni Mubarak, tun a shekarar 2012. Sai dai kotu ta bayar da belinsu bayan saka masu takunkumin cewar ba zasu fita daga kasar ba.

Kotun zata kara zama domin cigaba da sauraron karar a ranar 20 ga watan Oktoba.

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar tsohuwar minstar kudi, Kemi Adeosun, ta fice daga Najeriya kwana daya kacal bayan ta mika takardar barin mukaminta biyo bayan samunta da laifin karyar takardar bautar kasa.

DUBA WANNAN: An sayi hoton El-Rufa'i da wani dalibi ya zana cikin minti 2 a kan miliyan N2m

Adeosun ta kasance ministar kudin Najeriya tun watan Nuwamba na shekarar 2015. Ta yi murabus daga mukaminta ne bayan jaridar Premium Times ta bankado cewar ministar ta gabatar da takardar bauatr kasa ta bogi.

A jiya Jum'a, 14 ga watan Satumba, Mrs. Kemi Adeosun ta yi murabus daga kujerarta ta Ministar kudi, biyo bayan zarginta da ake yi na amfani da takardar shaidar yin bautar kasa ta bogi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng