An sayi hoton El-Rufa’i da wani dalibi ya zana cikin minti biyu a kan miliyan N2m

An sayi hoton El-Rufa’i da wani dalibi ya zana cikin minti biyu a kan miliyan N2m

- An sayar da wani hoto na gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, da wani dalibi ya zana a kan miliyan N2m

- Wani dalibin jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, Adebayo Seun, ya zana hoton cikin minti biyu

- Wani dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Mohammed Mamadi, ya sayi zanen da dalibin ya yi a wurin wani taro don matasa

A yau, Asabar, ne aka sayi wani zane na gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufa’i, da wani dalibin jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ya yi cikin minti biyu, a kan miliyan N2m.

Mamba a majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Mohammed Mamadi (mai wakiltar karamar hukumar Igabi), ne ya sayi zanen da dalibin ya yi a wurin wani taro da aka shirya domin karfafawa matasa gwuiwa a garin Kaduna.

An sayi hoton El-Rufa’i da wani dalibi ya zana cikin minti biyu a kan miliyan N2m
Hoton El-Rufa’i
Asali: Facebook

An sayi hoton El-Rufa’i da wani dalibi ya zana cikin minti biyu a kan miliyan N2m
Hoton El-Rufa’i
Asali: Facebook

Dalibin, Adebayo Seun, ya bayyana cewar bai taba samun kudi mai yawan haka ba daga basirar da Allah ya bashi ta zane.

Wani mai yin zane, Abubakar Umar, ya kara zana wani hoton na gwamna El-Rufa’I da fensil.

Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya taron ne domin zakulo matasa dake da basira a fanni daban-daban domin karfafa masu gwuiwa.

DUBA WANNAN: Barazana kan rayuwar Atiku: PDP ta yiwa APC gugar zana

Kwamishinan kasafi da tsare-tsare a jihar Kaduna, Muhammad Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar an shirya taron ne domin bawa matasa dammar tattauna kalubalen da suke fuskanta a yunkurinsu na inganta rayuwarsu domin gobe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel