Buhari zai ziyarci Katsina domin rufe gasar tseren Dawakai

Buhari zai ziyarci Katsina domin rufe gasar tseren Dawakai

Rahotanni daga jihar Katsina na nuni da cewar akwai kyakykyawan zaton cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci wasan karshe na tseren dawakai da zai gudana yau, Asabar, a garin Katsina.

Shugabannin da suka shirya gasar tseren dawakai da ake yi a Katsina sun bayar da tabbacin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda masoyin tseren doki ne, zai halarci bikin wasan tseren dawakai na karshe da za a yi a yau, Asabar.

Baya ga sa ran halartar shugaba Buhari, ana kyautata zaton cewar manyan sarakunan arewacin Najeriya da kuma manyan attijirai zasu halarci bikin rufe gasar na yau.

Alhaji usaman Nagogo, shugaban kwamitin shirya gasar, ya ce ana shirya gasar ne domin samun kudin da za a yi amfani das u wajen tallafawa rayuwar marasa karfi a jihar. Kazalika ya bayyana cewar gasar na da goyon bayan tsofin shugabannin kasar nan a mulkin soji da farar hula.

Buhari zai ziyarci Katsina domin rufe gasar tseren Dawakai
Buhari
Asali: Twitter

Za a fafata ne a wasan tseren na yau tsakanin tsakanin jihohi hudu da suka hada da Abuja, Bauchi, Minna da Zaria. Wasan zai matukar daukan hankalin ‘yan kallo saboda irin bajintar da jihohin 4 suka nuna a wasannin baya da suka fafata.

DUBA WANNAN: Allah ya yiwa jakadan Najeriya a kasar Qatar ya rasuwa

Wani wasa da shi ma ake ganin zai dauki hankali shine wanda za a kece raini tsakanin Jos da kuma Katsina, mai masaukin baki.

Wannan shine karo na farko da gasar ta samu halartar mahaya dawakai daga Jos.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel