Gwamnoni 7 dake hankoron Kujerun Sanata a Zaben 2019

Gwamnoni 7 dake hankoron Kujerun Sanata a Zaben 2019

A yayin da hankoron kujeru na majalisar dattawa ta zamto ruwan dare a tsakankanin gwamnonin kasar nan da suka kammala wa'adin su na shugabanci a jihohinsu, Legit.ng muku jerin wasu gwamnoni biyar dake neman sharar zagon na rayuwa a kujeru na Sanata.

Kamar yadda bincike na shafin jaridar The Punch ya bayyana, a halin yanzu akwai kimanin tsaffin gwamnoni 15 dake kan kujerunsu na Sanatoci a majalisar dattawa bayan sun kammala wa'adin shekaru takwas a kan kujerun gwamna da kundin tsarin mulkin kasar nan ya ba su dama.

Ko shakka ba bu mafi akasarin gwamnonin kasar nan na share zangon rayuwarsa a majalisar dattawa da kundin tsari ya yi tanadi na takarar kujerar Sanata ba tare da kayyade iyaka ba.

A yayin da babban zaben na 2019 ke ci gaba da karatowa, akwai wasu gwamnonin kasar nan da tuni suka bayyana kudirin su na neman takarar kujerun Sanata sakamakon kammala wa'adin su na shekaru takwas kan kujerun gwamna a jihohin su.

Gwamnoni 7 dake hankoron Kujerun Sanata a Zaben 2019
Gwamnoni 7 dake hankoron Kujerun Sanata a Zaben 2019
Asali: Depositphotos

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamann jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar kujerar sanatan jihar ta Tsakiya a zaben 2019 karkashin inuwa ta jam'iyyar APC.

Takwaransa na jihar Oyo, Abiola Ajimobi, tun a watan Fabrairun da ya gabata ya bayyana kudirin sa na neman tsayawa takarar kujerar Sanatan jihar ta Kudu yayin babban zabe na kasa.

Dukkanin gwamnonin biyu sun wakilci jihohin su a majalisar ta dattawa a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007 kafin dawowa kujerun gwamna a shekarar 2011 da ta gabata.

Gwamnan jihar Kwara, Ahmed Abdulfatai, a karshen makon da ya gabata ya yanki fam din bayyan kudirin sa na neman takarar kujerar Sanatan jihar ta Kudu a karkashin sabuwar jam'iyyarsa ta PDP.

KARANTA KUMA: Abdul aziz Yari Gwamna ne mai fuska biyu - Marafa

Baya ga Amosun, Ajimobi, Abdulfatai, akwai kuma gwamnonin jihohin Zamfara da Imo dake hankoron kujeru a majalisar dattawa yayin da suka kammala wa'adin su na shekaru takwas a akan karagar mulki.

A yayin da gwamnan Zamfara, Abudulaziz Abubakar Yari ke hankoron kujerar Sanatan jihar sa ta Yamma, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana kudirin tsayawa takarar kujerar Sanatan jihar sa sakamakon ajiye sha'awarsa ta takarar kujerar shugaban kasa.

Kazalika gwamnonin jihohin Yobe da Nasarawa; Ibrahim Geidam da kuma Umaru Tanko Al Makura, na da niyya da komawa kujeru a majalisar ta dattawa yayin zaben na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng