Farashin wasu kayayyaki a kasuwa ya yi tashin gwauron zabi bayan watanni 18 da faduwa

Farashin wasu kayayyaki a kasuwa ya yi tashin gwauron zabi bayan watanni 18 da faduwa

A ci gaba da duba yanayin farashin kayayyaki a kasuwannin kasar nan, Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da wani sabon rahoto a ranar Juma'a, 14 ga watan Satumba, in ta bayyana cewa farashin wasu kayyaki a kasar ya yi tashin gwauron zabi.

A watan Janairun shekara ta 2017 ne farashin kayayyakin ya dai-daita, wanda ya sanya tattalin arzikin kasar ya habbaka, sai dai bayan watanni 18 farashin kayayyakin ya sake tashi, wanda masana ke kallon hakan a matsayin barazana ga kasuwanci da tattalin arzikin kasar.

KARANTA WANNAN: Saboda in ceci rayukan jama'a yasa aka ganni rike da kwalbar giya ina aiki - Dan sanda

A cewar rahoton, farashin kayayyaki da kuma gudanar da ayyukan su a watan Augusta, ya haura daga kashi 11.14% zuwa kashi 11.23%.

Farashin wasu kayayyaki a kasuwa ya yi tashin gwauron zabi bayan watanni 18 da faduwa
Farashin wasu kayayyaki a kasuwa ya yi tashin gwauron zabi bayan watanni 18 da faduwa
Asali: Instagram

"Kididdigar Farashin kayayyakin da jama'a suka fi saye, (CPI) shekara zuwa shekara ya haura da kashi 11.23% a wannan watan na Augusta. Hakan ya sa farashin ya karu da kashi 0.09 idan aka alakanta shi da farashin watan Yulin 2018 (kashi 11.14), wanda hakan ta faru a cikin watanni 18 daga dai-daita farashin," a cewar rahoton.

Rahoton ya ce: "An samu hau-hawar farashin ne a sashen COICOP wanda ya ke a sahun farko na kididdigar. Idan aka duba kididdigar wata zuwa wata, sashen farko na farashin kididdigar ya karu da kashi 1.05 a watan Augustar 2018, la'akari da faduwarsa a watan Yulin 2018, in da aka samu kashi 1.13."

A wani labarin:

Wata babbar cibiyar bincike da kuma fitar da rahoto kan muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar kasashe, Forbes Africa, ta bayyana Nigeria a matsayin kasar da ta zamo zakaran gwajin dafi bayan da ta zarce sauran kasashen Afrika a fannin tattalin arzikin kasa a wannan shekarar ta 2018.

A baya bayan nan ne gwamnatin tarayya da sauran gwamnatocin kasar suka samu akalla zambar miliyan 7 (N7tn) a cikin watanni 11, kamar dai yadda rahoton Forbes ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel