2019: Dan takarar shugaban kasa ya bukaci a dakatar da Buhari

2019: Dan takarar shugaban kasa ya bukaci a dakatar da Buhari

- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NAC, Olapade Agoro ya yi suka kan siyawa Buhari fam din takara da NCAC ta yi

- Dr Agoro ya bukaci jam'iyyar APC ta bayyana sunayen wadanda suka sayawa Buhari fam tare da sana'oinsu da takardun harajinsu

- Dr Agoro ya yi barazanar maka INEC a kotu muddin bata tursasa wa APC ta bayyana sunayen wadanda suka siya wa Buhari fam ba

2019: Dan takarar shugaban kasa ya bukaci a dakatar da Buhari
2019: Dan takarar shugaban kasa ya bukaci a dakatar da Buhari
Asali: Twitter

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar National Action Council (NAC) Dr. Olapade Agoro ya yi barazanar gurfanar da hukumar zabe na kasa (INEC) da jam'iyyar APC a kotu saboda sayawa Buhari fam din takara da mambobin kungiyar (NCAC) su kayi.

A yayin da ya ke magana da manema labarai a jiya Alhamis, Agoro ya bukaci jam'iyyar APC ta bayyana sunayen mambobin NCAC da suka hada kudi har N45.5 miliyan domin siyawa shugaba Buhari fam kamar yadda New Nigeria ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari

Ya kuma yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta dakatar da shugaba Buhari daga takarar zaben 2019 har sai lokacin da APC da bayyana sunayen mambobin NCAC ga 'yan Najeriya.

A cewar dan takarar shugaban kasar na NAC, "Ba dai dai bane a demokradiyya wasu mutane saya wa shugaban kasa mai ci fam din takarar zabe lokacin da ya ke neman zarcewa kan karagar mulki."

Dr Agoro ya ce, "Yan Najeriya za su so sani sunayen mutanen da su kayi karo-karon kudi aka sayi fam din, sana'o'in da su keyi da kuma takardun biyan haraji na kasa."

Dr Agoro ya yi ikirarin cewa amincewa da kuma karbar fam din da Buhari ya yi alama ce da ke nuna yana goyon bayan rashawa saboda idan ya yi nasara a zabe dukkan wadanda suka bayar da kudade aka siya fam din za su dawo karbar kyautarsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel