Buhari ya yi hakuri da Saraki - Wata na hannun daman Obasanjo

Buhari ya yi hakuri da Saraki - Wata na hannun daman Obasanjo

- Sanata Florence Ita-Giwa, ta yabi shugaba Muhamamadu Buhari game da yadda ya ke nuna dattaku da hakuri kan dambarwar da ke tsakanin majalisa da fadar shugaban kasa

- Ita-Giwa ta ce idan da lokacin shugaban kasa da suka shude ne da Bukola Saraki ba zai wuce shekara daya a kujerarsa ba

- Ita-Giwa ta shawarci fadar shugaban kasa da majalisa su mayar da takubbansu suyi aiki tare saboda cigaban Najeriya

Tsohuwar hadiman shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, Sanata Florence Ita-Giwa ta yabi shugaba Muhammadu Buhari saboda dattaku da kamun kai game da irin dambarwar da ke faruwa tsakanin fadar shugaban kasa da majalisar tarayya kamar yadda This Day ta wallafa

Sanata Ita-Giwa ta ce matsalar da ke tsakanin majalisar da fadar shugaban kasa ba sabon abu bane domin tsakanin 1999 zuwa 2003, lamari mai kama da wannan ya faru lokacin da Chuba Okadigbo ya zama shugaban majalisa ba da son fadar shugaban kasa ba bayan an tsige Evans Enwerem.

Buhari ya yi hakuri da Saraki - Inji na hannun daman tsohon shugaba Obasanjo
Buhari ya yi hakuri da Saraki - Inji na hannun daman tsohon shugaba Obasanjo
Asali: Twitter

Sai dai banbancin abinda ya faru a wancan lokacin da yanzu shine irin matakan da shugabanin kasa suka dauka.

DUBA WANNAN: Wani Sanata ya bukaci kotu ta aika Saraki gidan yari

"A matsyina na wanda tayi aiki da tsaffin shugabanin kasa biyu, ina ganin shugaba Buhari yana da dattaku da hakuri domin inda da lokacin tsaffin shugabanin kasar ne da wuya shugaban majalisar zai yi shekara daya kan mulki kafin a tsige shi," inji Ita-Giwa.

Ita Giwa ta kara ta cigaba da cewa ta fuskanci tsangwama da matsin lamba saboda a wannan lokacin ta goyi bayan Okadigbo.

"An tsige ni daga mukamin mataimakiya shugaban marasa rinjaye, an bani gida a dokan daji a kauyen Apo inda namun daji ke kawo farmaki gida na. Anyi kara ta a majalisa saboda na gina katanga kuma ya sanya majalisa ta biya kudin. Anyi kara ta a kotu kan abubuwa da yawa kawai domin na goyi bayan Okadigo."

Ita-Giwa ta shawarci fadar shugaban kasa da majalisa suyi sulhu su rika aiki tare domin hakan shine yafi alheri ga talakawan Najeriya.

Ta ce a lokacin da ta ke aiki a matsayin mai bayar da shawara na musamman ga shugaban kasa, ta kan shirya taro na musamman tsakanin fadar shugaban kasa da majalisa kuma hakan ya taimaka wajen kawo hadin kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel