PDP ce za ta yi nasara a Zaben 2019 - Kwankwaso

PDP ce za ta yi nasara a Zaben 2019 - Kwankwaso

Fitaccen dan siyasar nan na Arewa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa jamiyyar su ta adawa ta PDP ita ce za ta yi nasara a dukkan kujerun siyasa yayin babban zabe na 2019.

Kwankwaso wanda ya samu kyakkyawar tarba ta dubunnan al'umma sanye da jajayen huluna yayin da ya isa birnin Makurdi na jihar Benuwe da tsakar ranar Alhamis din da ta gabata, ya bayyana cewa ya ziyarci jihar ne domin yabawa Gwamna Samuel Ortom kan sauyin shekarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

A yayin yabawa wannan kyakkyawar shawara da gwamnan ya yanke ta sauyin sheka, Kwankwaso ya kuma bayyana cewa ya ziyarci jihar ne domin kara karfin alaka da dangantaka tsakaninsa da gwamnan da kuma masu ruwa da tsaki na jam'iyyar kan kudirin sa na neman kujerar shugaban kasar nan.

PDP ce za ta yi nasara a Zaben 2019 - Kwankwaso
PDP ce za ta yi nasara a Zaben 2019 - Kwankwaso
Asali: UGC

Kazalika Kwankwaso ya bayyana cewa, gwamnatin jam'iyyar APC ta gaza ta kowane bangare ta fuskar jagoranci a kasar nan da ba bu wani bambanci tsakanin shekaru ukun da tayi akan karagar mulki da shekaru 16 na shugabancin jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Shirin N-Power ya samar da abin yi ga Matasa 500, 000 a Najeriya - Osinbajo

Sanatan Kano ta Tsakiya ya kuma bayyana takaicin sa dangane da yadda gwamnatin jam'iyyar APC ta yi sanadiyar mummunan rabuwar kai a tsakanin al'ummar kasar nan da ba a taba samun makamancinsa ba a tarihinta.

Ya kuma lashi tsinin takobi da cewar al'ummar kasar nan ba za su taba da na sanin zaben sa ba a sanadiyar kyakkyawan jagoranci da za su fuskanta na bunkasar jin dadin su da kuma ci gaban kasa baki daya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnan na jihar Benuwe ya bayyana cewa rikici na ta'addanci ya salwantar da rayukan mutane 560 cikin watanni 9 kacal a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel