Magoya bayan Dogara sun saya masa tikikin takara ta jam'iyyar PDP

Magoya bayan Dogara sun saya masa tikikin takara ta jam'iyyar PDP

- Wasu daga cikin magoya bayan Kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara, sun saya masa fam din takarar a PDP

- Sun ce sun saya masa fam din ne saboda suna son ya dawo PDP duba da rashin adalcin da APC ke masa

- Dogara ya yi godiya garesu inda ya bukaci su bashi lokaci ya yi shawara da magoya bayansa na APC kafin ya cike fam din

Daruruwan mogaya bayan Kakakin majalisar dattawa, Hon. Yakubu Dogara daga yankunan Bogoro/Dass/Tafawa Balewa na jihar Bauchi sun gabartawa Dogara fom din takarar jam'iyyar PDP, inda suka roki shi ya fice daga APC.

Mutanen wanda a kalla sun kai 1000 sun zaiyarci gidan Dogara da ke Abuja a yau Alhamis, sun ce sun yanke shawarar siya masa fam din takarar Sanata a PDP ne saboda irin rashin adalcin da ake masa a jam'iyyar APC.

Magoya bayan Dogara sun saya masa tikikin takara ta jam'iyyar PDP
Magoya bayan Dogara sun saya masa tikikin takara ta jam'iyyar PDP
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yiwa mutane kisan kiyashi a Zamfara

Jagororin tawagar, Hon. Mohammed Aminu Tukur, Alhaji Adamu Jambil da Mrs Saleh da su kayi magana a madadin yankunansu sunce sunan sabuwar jam'iyyar su Dogara Peoples Party kuma za su bi shi duk jam'iyyar da ya shiga.

A jawabinsa, Hon. Aminu Tukur ya ce jam'iyyar APC ta zama na kama karya da rashin adalci a maimakon adalci da shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin zai yiwa dukkan 'yan jam'iyyar.

A bangarensa, Dogara ya shaidawa dandazon magoya bayansa cewa ya saurari shawarwarinsu inda ya kara da cewa shi ba sabon shiga bane a siyasa.

Ya ce ko anyi musu adalci ko akasin haka, suna da hankulansu kuma za su banbance tsakanin wadanda ke son daraja su da wadanda ke son muzanta su.

Dogara ya mika godiyarsa game da fam din da suka kawo masa sai dai ya ce su bashi lokaci ya yi shawara da magoya bayansa na APC kafin ya bayyana matakin da zai dauka. Ya kuma ce yana alfahari da mutanensa shi yasa baya zuwa wajen kowa rokon wata alfarma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel