Magoya bayan Shugaba Buhari sun kashe wani Bawan Allah a Kaduna

Magoya bayan Shugaba Buhari sun kashe wani Bawan Allah a Kaduna

Mun ji cewa wasu Bayin Allah da ke tsabar son Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun aika wani mutumi a cikin Tawagar tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku lahira bayan sun rutsa shi da jifa.

Magoya bayan Shugaba Buhari sun kashe wani Bawan Allah a Kaduna
‘Yan a mutun Buhari sun rutsa wani da duwatsu har ya mutu
Asali: Depositphotos

A cikin makon nan ne mu ka samu labari cewa wasu Magoya bayan Buhari sun kashe wani Direba har lahira bayan sun jefe sa a lokacin da ya tuko Tawagar tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar zuwa cikin Kaduna.

Kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar Rariya, wani Bawan Allah da ke tare da mutanen Atiku Abubakar mai suna Aminu Adam ya gamu da ajalin sa a hannun ‘Yan adawar ‘Dan takarar na Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.

Wannan Matashin Direba ya hadu da mutuwar sa ne a lokacin da Tawagar Atiku Abubakar ta shiga Kaduna wajen wani daurin aure da aka yi kwanaki. Atiku da mutanen sa sun hadu da ‘Yan a-mutun Buhari wajen wannan taron biki.

KU KARANTA: Kotu ta sa a yiwa wani bulala saboda yada fitina a unguwarsu

Yanzu dai mun samu labari maras dadi cewa wannan Saurayin Direba mai shekaru 29 a Duniya yace ga garin ku nan bayan da wadannan Masoyan masu ihun sai Shugaba Buhari su kayi masa ature da duwatsu kurum saboda banbancin siyasa.

A jiya ne ‘Dan takarar kujerar Shugaban kasar a karkashin Jam’iyyar adawa na PDP watau Atiku Abubakar ya kai ziyara zuwa Jihar Katsina inda nan ne Mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya kuma soki Gwamnatin sa.

Atiku yana cikin masu neman takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin Jam’iayyar adawa ta PDP. A makon nan ne dai masu neman takarar a PDP su ka hadu a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel