Matsayi: Gwamnatin Amurka ta maye gurbin alkalin kasar da wani dan Najeriya
- Gwamnan jihar Washington, Jay Inslee, ya maye gurbin alkalin kotun lardin Snohomish County, George Bowden, da wani dan Najeriya, Edirin Okoloko
- Gwamna Islee ya nada Okoloko ne bayan alkali Bowden ya yi ritaya daga aiki
- An haifi Okoloko a Najeriya kuma ya yi karatun ilimin shari’a a jami’ar Benin dake jihar Edo
Gwamnan jihar Washington ta kasar Amurka, Jay Islee, ya nada wani dan asalin Najeriya, Edirin Okolok, a matsayin sabon alkalin kotun lardin Snohomish County bayan ritayar alkalin kotun, George Bowden.
Okoloko ya shafe shekaru 13 yana aiki a sashen cin mutuncin yara, manya da mata a kotun ta lardin Snohomish County.
Nadin Okoloko ya biyo bayan irin nasarar da ya samu a laifukan da ya jagoranci gurfanar da wadanda suka aikata su yayin da yake aiki a sashen gurfanar da masu laifi a kotun ta Snohomish County.
An haifi Okoloko a Najeriya kuma ya yi karatun ilimin shari’a a jami’ar Benin dake jihar Edo kafin daga bisani ya samu shaidar zama lauya daga makarantar horon lauyoyi dake Seattle a kasar Amurka.
DUBA WANNAN: 2019: Da gan-gan APC ta zuga kudin fam don mu kasa saya - Dan takarar shugaban kasa
A wani labarin na Legit.ng kun karanta cewar gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya amince da fitar da biliyan N19.8bn adomin biyan ma’aikata da ‘yan fansho bashin hakkokinsu da suke bin jihar na tsawon wata 4.
A sanarwar da kwamishinan kudi na jihar Osun, Bola Oyebamiji, ya bayar a yau, Talata, y ace gwamna Rauf Aregbesola ya amince da fitar da biliyan N19.8bn domin a biya ma’aikata da ‘yan fansho bashin albashin wata 4 da suke bin jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng