Namu ta samu: Wata 'yar Arewa ta samu babban mukamin kasa-da-kasa

Namu ta samu: Wata 'yar Arewa ta samu babban mukamin kasa-da-kasa

- Wata 'yar Arewa ta samu babban mukamin kasa-da-kasa

- Sunan ta Farfesa Hauwa Ibrahim

- Farfesa Hauwa yar asalin jihar Bauchi ce

Wata 'yar Najeriya daga bangaren arewacin kasar mai suna Farfesa Hauwa Ibrahim ta samu babban mukami da wata kungiyar dake ayyukan ta a kasashe da kuma ke zaune a garin birnin Paris dake rajin tabbatar da samun sahihiyar demokradiyya da kuma labarai masu inganci.

Namu ta samu: Wata 'yar Arewa ta samu babban mukamin kasa-da-kasa
Namu ta samu: Wata 'yar Arewa ta samu babban mukamin kasa-da-kasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Wasu masana daga Landan sun yi hasashen faduwar Buhari zaben 2019

Majiyar mu ta Daily Nigerian ta samu cewa ita dai Farfesa Hauwa yar asalin jihar Bauchi ce kuma babbar Lauya ce da ta lashe kyautar hazaka a shekarar 2005 ta sashen Najeriya watau European Parliament’s Sakharov Prize (Nigeria) a turance.

Legit.ng ta samu cewa ita dai Farfesa Hauwa Ibrahim kafin samun mukamin nata, tana koyawa a makarantar gaba da Sakandare ta Saint Louis University School of Law da kuma Stonehill College dukkan su a kasar Amurka.

Haka ma dai Farfesar ta rike mukamai da dama a kasashe da yawa inda ta samu lambobin girma da shaida mai kyau.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ana sa ran zai jagoranci tawagar 'yan Najeriya zuwa taron majalisar dinkin duniya karo na 73 da za'a gudanar a garin New York na kasar Amurka nan ba da dadewa ba.

Kamar yadda muka samu, ministan harkokin waje na Najeriya Mista Geoffrey Onyeama shine ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Abuja ranar Talatar da ta gabata inda kuma yace taron za'a gudanar da shi ne a ranar 18 ga watan Satumbar da muke ciki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel