Babbar magana: Jonathan ya saka ayar tambaya a kan lafiyar hankalin Oshiomhole

Babbar magana: Jonathan ya saka ayar tambaya a kan lafiyar hankalin Oshiomhole

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya saka ayar tambaya a kan lafiyar hankalin shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole

- Jonathan ya yi wannan kalami ne a matsayin martani ga Oshiomhole a kan batun zargin sayen kuri’u lokacin zabe

- Tsohon shugaban kasar ya ce Oshiomhole na yin barin zance ne saboda matsalolin da suka dabaibaye ofishinsa

Tsohon shugaban kasa Goodluck jonathan ya saka alamar tambaya a kan lafiyar hankalin shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole. Jonathan na wannan kalami ne a matsayin martini ga kalaman Oshiomhole na cewar a lokacin mulkinsa ne aka fara amfani da kudi domin sayen kuri’ar masu zabe.

A wani jawabi da Jonathan ya raba ga manema labarai yau, Laraba, a Abuja ya ce bai san dalilin da yasa Oshiomhole zai yi kalaman karya a kansa ba. Tsohon shugaban kasar ya ce Oshiomhole na yin barin zance ne saboda matsalolin da suka dabaibaye ofishinsa.

Babbar magana: Jonathan ya saka ayar tambaya a kan lafiyar hankalin Oshiomhole
Jonathan da Oshiomhole
Asali: Depositphotos

Jonathan ya ce an fara sayen kuri’un masu zabe ne a zaben jihar Edo na 2016, shekara daya bayan ya bar ofis.

Ni ina ganin ya rude ne, domin zai yabe ka a yauidan kana APC amma gobe ya kushe ka gobe idan ka fita daga jam’iyyar .

DUBA WANNAN: Sabon salo: PDP ta zo da sabon tsari a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa

“Hatta ‘yan jam’iyyarsa bai kyale ba domin ko a yanzu haka akwai matsala tsakaninsa da wasu manyan jami’an gwamnatin APC irin su ministan kwadago, Chris Ngige. Halayensa kadai sun isa su rusa jam’iyyar APC,” a cewar kalaman na Jonathan da mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Ikechukwu Eze, ya saka hannu a kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel