Hadimin Gwamnan Jihar Filato ya yi gamo da ajali a Kasar India

Hadimin Gwamnan Jihar Filato ya yi gamo da ajali a Kasar India

Wani rahoto mai cike da ban al'ajabi gami da ban tausayi ya bayyana cewa, ajali ya katse hanzarin Emmanuel Samuel Nanle, babban hadimi na musamman kan harkokin hulda da manema labarai ga gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito, Nanle ya riga mu gidan gaskiya ne da sanyin safiyar yau ta Laraba, 12 ga watan Satumba a wani asibiti dake can kasar India.

Bambance-bambancen rahotanni daga fadar gwamnatin sun bayyana cewa, Nanle ya yi gamo da ajali ne a sakamakon bugun zuciya yayin da wasu ke ikirari ya ce ga garin ku nan sakamakon wata cutar daji da damki 'ya'yan hanji dake cikin Tumbin sa.

Sai daya daga cikin 'yan uwansa ya kawar da shakku inda ya bayyana cewa, Marigayi Nanle ya sha fama da rashin lafiya ta cutar daji a cikin Tumbinsa yayin da har a shekarar da ta gabata ya jinya a wani Asibiti dake birnin Jos.

Marigayi Emmanuel Nanle
Marigayi Emmanuel Nanle
Asali: Facebook

Mark Longyen, wani babban hadimi na musamman ga gwamnan jihar, shine ya bayar da tabbacin wannan rahoto yayin ganawarsa da manema labarai a fadar gwamnatinsu tare da bayyana yadda aka shilla da marigayi Nanle zuwa kasar ta India makonni biyu da suka gabata.

KARANTA KUMA: Wasu Manema Takarar Kujerar Gwamna 2 sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Benuwe

Rahotanni sun bayyana cewa, kafin ajali ya cimma marigayi Nanle, ya kasance dan asalin karamar hukumar Panshik ta jihar inda ya rike mukamai na jagoranci kungiyoyi daban-daban na matasa.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnan Lalong ya bayyana cewa tuni wadanda suka kai hari kan wasu yankunan jihar sun shiga hannun hukuma inda za su fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel