Ko PDP ba ta bani tuta ba sai na yi kokarin ganin Buhari ya sha kasa - Atiku

Ko PDP ba ta bani tuta ba sai na yi kokarin ganin Buhari ya sha kasa - Atiku

A jiya ne ‘Dan takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawa na PDP watau Atiku Abubakar ya kai ziyara zuwa Jihar Katsina inda nan ne Mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ko PDP ba ta bani tuta ba sai na yi kokarin ganin Buhari ya sha kasa - Atiku
Atiku Abubakar ya ziyarci Mahaifar Shugaba Buhari Ranar Talata
Asali: Facebook

Atiku Abubakar ya bayyana cewa dole Gwamnatin Buhari ta tafi a lokacin da ya gana da manyan PDP a Sakatariyar Jam’iyyar adawar da ke cikin Garin Katsina. Atiku ya nuna cewa Shugaba Buhari ya nakasa tattalin arzikin kasar nan.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya kuma nuna cewa Gwamnatin Buhari ta jefa jama’a cikin yunwa da rashin aikin yi. Atiku dai ya zargi tsare-tsaren Shugaba Buhari da saka mutanen kasar nan cikin kangi da mugun wahala.

Atiku ya tunawa Jama’a cewa har yanzu ana fama da rashin tsaro ta bangaren Boko Haram da kuma satar mutane. Ban da wannan dai, ‘Dan takarar yace wannan Gwamnati ta raba kan al’ummar kasar nan don haka dole a sake zabi.

KU KARANTA: Za mu cigaba da maganin Barayin Gwamnati - Buhari

Wani tsohon Sanatan Bauchi ta tsakiya a karkashin Jam’iyyar PDP watau Abdul Ningi dai ya nuna cewa Atiku ne kadai zai iya ja da Gwamnatin Shugaba Buhari a zaben 2019 har ya ba ta ciwon kai don haka yake ganin PDP ta ba sa tuta.

Alhaji Atiku ya kara tabbatar da cewa ko da ya sha kasa a zaben fitar-da-gwani, zai cigaba da zama a Jam’iyyar PDP tare da yin bakin-kokarin sa wajen ganin duk wanda aka tsaida ya tika Shugaba Muhammadu Buhari da kasa a zaben 2019.

Kwanaki kun ji cewa Atiku yayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaba Buhari inda yace daga 2015 zuwa yanzu Gwamnatin APC ta samu fiye da Dala Biliyan 120 daga man fetur kuru amma a banza.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel